Ijeoma Queenth Daniels
Ijeoma Queenth Daniels (An haife ta a ranar 25 ga ga watan Satumba 1992) ta kasance yar wasan kwallan kafa ce a Nijeriya, wacce ke taka rawar gani a kulub din Adana İdmanyurduspor, tana buga gasan kwallan kafa na mata mai suna Turkish Women's First Football League, tana saka lamban riga 56.[1][1]
Ijeoma Queenth Daniels | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Najeriya, 25 Satumba 1992 (32 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya |
Kariyanta a wasanni
gyara sasheDaniels ta koma Turkiyya ne a watan Nuwamba na shekarar 2015, kuma ta koma kungiyar Ataşehir Belediyespor da ke Istambul, don ta halarci gasan a kakar wasannin farko ta Mata a shekarar 2015 zuwa shekarar 2016 . Ta buga wasanni takwas kuma ta ci kwallo daya. A kakar wasa mai zuwa, ta sanya hannu ma kulub din Kireçburnu Spor, inda ta buga wasanni takwas kawai a cikin yanayi daya da rabi. A rabin shekaru na biyu na Lokacin 2017–18, ta sauya sheka zuwa İlkadım Belediyesi Yabancılar Pazarı Spor dake Samsun, inda ta fito ata buga wasanni biyu. A rabi na biyu na kakar Wasannin Farko ta Mata ta shekarar 2019 zuwa 2020, ta koma kulub din Adana İdmanyurduspor.[2]
Jin ciwo
gyara sasheA ranar 4 ga watan Disambar shekarar 2016, ta ji rauni yayin wani wasa, taji ciwon ta yi yunƙurin tafiya dan ta fita daga filin, amman ta kasa tafiya. Wata yar wasan kungiyar kwallan kafa ce ta dauke ta a bayan ta mai suna Aysun Aliyeva, yar wasan kungiyar adawa ce na kulub din Antalya Spor, tafi Daniels saukin kai, ta dauke ta a kan raha sannan ta kaita benci.[3]