Ibrahim Khalil Umar masanin kimiyyar Najeriya ne kuma shugaban jami'a. Ya kasance mataimakin shugaban jami'ar Bayero Kano, Nigeria daga shekarar 1979 zuwa 1986.[1] Yana da B, Sc. a fannin Physics da lissafi daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Najeriya, a M. Sc. a fannin kimiyyar lissafi daga Jami'ar Arewacin Illinois, Amurka da Ph.D. (1974) a fannin kimiyyar lissafi a Jami'ar Gabashin Anglia, United Kingdom.[2] A shekarar 1976 ya zama ɗan Najeriya na farko a fannin kimiyyar lissafi da ya koyar a Jami’ar Bayero.[3] A shekara ta 1978 ya yi aiki a majalisar tsarin mulki ta ƙasa wadda ta tsara kundin tsarin mulkin jamhuriya ta biyu.[4]

Ibrahim Umar
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Mutuwa 30 ga Janairu, 2023
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
University of East Anglia (en) Fassara
Northern Illinois University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a Malami da malamin jami'a
Prof. Ibrahim H. Umar

A tsakanin shekarar 1994 zuwa 1997, Umar ya zama shugaban jami'ar fasaha ta tarayya, Minna.[5]

Ya wakilci Najeriya a Majalisar zartarwa ta Majalisar Makamashi ta Duniya daga 1990. Ya kasance memba na tawagar Najeriya zuwa babban taron Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) daga 1989 kuma an naɗa shi Darakta-Janar na Hukumar Makamashi ta Najeriya a shekara ta 1989. Ya yi aiki a matsayin Shugaban Hukumar Gwamnonin IAEA a tsakanin shekarar 2000-2001. A shekara ta 2004 ya kasance Daraktan Cibiyar Bincike da Horar da Makamashi, inda aka fara gudanar da bincike kan makamashin nukiliya a Najeriya.[6]

A cikin shekarar 2007, ya kasance a cikin kwamitin ba da shawara na ƙasa da ƙasa don taron ƙasa da ƙasa kan Sabunta Makamashi don ci gaba mai ɗorewa a Afirka, wanda aka gudanar a Jami'ar Najeriya, Nsukka a Najeriya.[7]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2008-01-10. Retrieved 2023-03-07.
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2007-09-25. Retrieved 2023-03-07.
  3. https://dailypost.ng/2014/12/27/kano-elders-forum-appoints-professor-ibrahim-umar-new-chairman/
  4. https://prnigeria.com/2014/12/27/kano-elders-forum-appoints-prof-ibrahim-umar-new-chairman/
  5. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-10-26. Retrieved 2023-03-07.
  6. https://www.energy.gov.ng/index.php?option=com_content&task=view&id=7&Itemid=58
  7. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2009-06-02. Retrieved 2023-03-07.