Ibom E-Library ɗakin karatu ne da ke Uyo, Jihar Akwa Ibom, Najeriya. Laburare wanda mallakar gwamnati shine nau'in dijital na farko a Yammacin Afirka. Hakanan Ibom e-library na ɗaya daga cikin manyan ɗakunan karatu a Afirka. [1]

Ibom E-Library
digital library (en) Fassara
Bayanai
Farawa 2012
Ƙasa Najeriya
Street address (en) Fassara IBB Ave, 520102, Uyo, Akwa Ibom
Wuri
Map
 5°00′56″N 7°54′46″E / 5.01549765°N 7.91279384°E / 5.01549765; 7.91279384
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJahar Akwa Ibom

An kaddamar da ɗakin karatun ne a garin Uyo dake jihar Akwa Ibom a ranar 25 ga watan Satumba 2007 ƙarƙashin gwamnatin tsohon gwamna Godswill Akpabio. [2] An yi ta ne a kan titin Ibrahim Babangida a jihar. [3]

Laburaren Ibom wani haɗaɗɗen wuri ne na zamani tare da kayan aiki masu ban sha'awa waɗanda ke taimakawa ilimi da bincike na ilimi. Yana da ikon ɗaukar mutane 1000, ɗakin karatu ya kasu kashi na sirri da buɗewa da ɗakunan allo da ofisoshi [4] [2]

Tari (collection)

gyara sashe

Laburaren Ibom ya ƙunshi cibiyar albarkatun kayan aikin multimedia don yara, wasannin ilimi 1260 da kayan aikin lissafi 1000. [5] Yana da abubuwa sama da 30,000 waɗanda suka shafi adabi da kayan aiki don taron e-conferencing.

Duba kuma

gyara sashe

Dakunan karatu a Najeriya

Manazarta

gyara sashe
  1. Oluka, Peter (2018-04-19). "Akwa-Ibom e-library surpasses 4million subscribers". TechEconomy.ng (in Turanci). Retrieved 2022-07-17.[permanent dead link]
  2. 2.0 2.1 "E-Library places Uyo at advantage, says Gov Akpabio". Vanguard News (in Turanci). 2013-03-19. Retrieved 2022-05-19.
  3. TheMail (2020-08-25). "Investigation: The story of the Rise and Fall of Ibom e-library - The Mail Newspaper" (in Turanci). Retrieved 2022-05-19.
  4. "Stakeholders Make Case for Optimum Use of A'Ibom E-Library". Independent Newspaper Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-05-19.
  5. "Akwa Ibom e-library finally opens, with a fee - Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2012-12-17. Retrieved 2022-05-19.