Godswill Akpabio
Godswill obot AKpabio Con (an haife shi ranar 9 ga watan Disamba, shekarar 1962) ɗan siyasa ne na Najeriya kuma ɗan siyasa ne a halin yanzu shine Shugaban majalisar Dattijai ta 10 a Najeriya. Ya yi aiki a matsayin Sanata mai wakiltar Akwa Ibom Arewa maso Yamma daga shekara ta, 2015 zuwa 2019 da kuma 2023. Ya kuma rike mukamin minista a harkokin Neja Delta daga Shekara ta, 2019 zuwa 2022. Yayi gwamnan jihar Akwa Ibom daga shekara ta, 2007 zuwa 2015.[1]
Godswill Akpabio | |||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
13 ga Yuni, 2023 - ← Ahmed Ibrahim Lawan
25 ga Faburairu, 2023 - ← Christopher Stephen Ekpenyong District: Akwa Ibom North-West Senatorial District
21 ga Augusta, 2019 - 11 Mayu 2022 ← Usani Uguru Usani - Umana Okon Umana →
ga Yuni, 2015 - ga Yuni, 2019 District: Akwa Ibom North-West Senatorial District
29 Mayu 2007 - 29 Mayu 2015 ← Victor Attah - Udom Gabriel Emmanuel → District: Akwa Ibom North-West Senatorial District | |||||||||||
Rayuwa | |||||||||||
Haihuwa | 19 Disamba 1962 (61 shekaru) | ||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||
Ƙabila | Mutanen Ibibio | ||||||||||
Harshen uwa | Harshen Ibibio | ||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||
Abokiyar zama | Ekaette Unoma Akpabio | ||||||||||
Karatu | |||||||||||
Makaranta |
Jami'ar Calabar Makarantar Koyan Lauya ta Najeriya Kwalejin Gwamnati Umuahia | ||||||||||
Harsuna |
Turanci Harshen Ibibio Pidgin na Najeriya | ||||||||||
Sana'a | |||||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||||
Imani | |||||||||||
Jam'iyar siyasa |
All Progressives Congress All Progressives Congress |
Karatu da Aiki
gyara sasheAkpabio ya yi karatu a Makarantar Firamare ta Methodist, Ukana, Essien Udim LGA, Jihar Akwa Ibom; a Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Port Harcourt, Jihar Rivers; da Jami'ar Calabar, Jahar Cross River, inda yayi digiri a fannin shari'a a makarantar. Gyaran sana'a da aiki
Aiki
gyara sasheMatsayin malami kuma a matsayin abokin hulda da jama'a tare da Paul Usoro & Co., wani kamfanin doka ne a Najeriya.
Mukamin Gwamnati
gyara sasheA shekarar, 2002, Gwamna Obong Victor Attah ya nada shi Honourable Commissioner na Man Fetur da Albarkatun kasa a jihar Akwa Ibom. Tsakanin shekara ta, 2002 zuwa 2006, ya yi aiki a matsayin kwamishina a ma'aikatu uku masu mahimmanci: Man Fetur da Albarkatun ƙasa, Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, da Filaye da Gidaje.
Siyasa
gyara sasheA shekara ta, 2006, ya yi sha’awar tsayawa takarar gwamna a jihar Akwa Ibom a zaɓen fidda gwanin da aka fafata tare da doke wasu ‘yan takara 57 da suka yi takara a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).Yaƙin neman zaɓen da ya yi mai taken, “a yi nufin Allah” ya sami goyon bayan jama’a kuma aka zaɓe shi Gwamna a shekarar, 2007. An sake zaɓen shi a karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Akwa Ibom a shekarar, 2011.
a shekarar, 2013, an zabe shi a matsayin Shugaban sabuwar kungiyar Gwamnonin PDP.
Takarar Sanata
gyara sasheA shekarar, 2015, ya tsaya takarar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma (Ikot Ekpene) don wakiltar gundumar a Majalisar Dattawan Tarayyar Najeriya. Da yake takara a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), ya samu kuri’u 422,009 daga cikin 439,449 inda ya doke Cif Inibehe Okorie na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 15,152 da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana. An zaɓi Akpabio a matsayin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa wanda ya fito daga Kudu-maso-Kudu a Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda jam’iyyar PDP ta amince da shi a Majalisar Dattawa kuma Shugaban Majalisar Dattawa ya bayyana shi a matsayin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa ranar 28 ga Yuli shekara ta,2015. PDP ta rasa rinjaye a hannun jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben shekara ta,2015.
A watan Agustan shekara ta,2018, ya yi murabus a matsayin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattijai, bayan ya sanar da sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress. Ya sauya sheka ya yi gangamin siyasa a mahaifarsa a filin wasa na garin Ikot Ekpene, jihar Akwa Ibom. A watan Yulin shekara ta, 2019 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabe shi kuma majalisar dattawan Najeriya ta tantance shi domin a nada shi minista. A ranar 21 ga Agusta shekara ta, 2019, an rantsar da shi a matsayin ministan harkokin Neja Delta.
A watan Yunin shekara ta,2022, Akpabio ya yi murabus daga mukaminsa na ministan harkokin Neja Delta domin ya tsaya takara a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki amma ya sauka a daren da aka gudanar da zaben fidda gwani wanda Bola Tinubu ya lashe. Kwanaki kadan bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa, ya fito a matsayin dan takarar Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma. Sai dai kuma yana cike da zarge-zargen da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar ke yi. Ya kayar da abokin hamayyarsa Emmanuel Enoidem na jam’iyyar Peoples Democratic Party ya zama zababben Sanata a zaben shekara ta,2023 inda ya samu kuri’u 115,401, inda Enoidem ya samu kuri’u 69,838.[2]
A ranar 13 ga watan Yunin shekara ta, 2023 ne aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar dattawan Najeriya da kuri'u 63 inda ya doke Sanata Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara wanda ya samu kuri'u 46.