Alhaji Hassan Wayam (an haife shi a shekarar alif 1956 ya kuma rasu a shekara ta alif 2020). ɗan asalin jihar Sokoto ne amma yayi duk rayuwarshi a garin Zaria jahar Kaduna. shahararren mawaƙin gargajiya ne na Hausa.[1]

Hassan Wayam
Rayuwa
Haihuwa Maradun, 1956 (67/68 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a mawaƙi

Tarihin sa

gyara sashe

An kuma haifi Alhaji Hassan Wayam a wani gari mai suna Gwadda, wanda kuma ake kira Bakin Ruba, a ƙasar Maradun ta Jihar Zamfara, a cikin shekara ta 1956.[2]

Mahaifin sa, Malam Muhammadu, Babarbare ne. Mahaifiyar sa Halima, Bafulatana ce. Sana’ar mahaifinsa ita ce sassaƙa, to amma kuma wani lokaci ya kan yi wa Fulani kiɗan kotso jefi-jefi.[3]

Ali Barau ya kai Wayam Zariya a cikin shekara ta 1969, ya aje shi a gidan sa da ke Unguwar Kanawa. Duk yamma sai ya ɗauke shi ya kai shi.

Manazarta

gyara sashe