Harin cocin Owo
A ranar 5 ga watan Yunin 2022, wani harin bam da aka kai a cocin Katolika da ke garin Owo a jihar Ondo a Najeriya. Akalla mutane 40 ne aka kashe,bayan faruwar harin anyi ƙiyasin kusan sun kai 80 waɗanda suka rasa rayukansu.[1] Wasu daga cikin gwamnatin tarayyar Najeriya na zargin ƙungiyar IS da ke yammacin Afirka da aikata kisan kiyashi.
| ||||
Iri |
harin ta'addanci mass shooting (en) Garkuwa da Mutane bomb attack (en) | |||
---|---|---|---|---|
Kwanan watan | 5 ga Yuni, 2022 | |||
Wuri | Owo | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Adadin waɗanda suka rasu | 50 | |||
Adadin waɗanda suka samu raunuka | 61 | |||
Hashtag (en) | #owomassacre, #OwoAttack da #OndoMassacre |
Bayan fage
gyara sasheJihar Ondo jiha ce mai zaman lafiya a kudu maso yammacin Najeriya. Yawancin sassann ƙasar nan[2] suna fama da rikice-rikice marasa ƙarfi, ciki har da tada kayar bayan Boko Haramm mafi yawa a arewa maso gabas, da kuma rikici da 'yan fashi a arewa maso yamma, dukansu sun cigaba fiye da shekaru goma. A shekarar 2021 ne aka fara wani tashin hankali na daban a yankin kudu maso gabas ƙarƙashinn jagorancin masu fafutukar kafa kasar Biafra. An samu ƙaruwar tashe-tashen hankula aa tsakanin manoma da makiyaya a Ondo kafin kisan kiyashin,[3] kuma a kwanakin baya gwamnatin jihar ta sanya dokar hana kiwo.[4]
Harin
gyara sasheAn kai harin ne a cocinn St. Francis Xavier Catholic Church da ke karamar hukumar Owo kuma an fara kai harin ne da misalinn karfe 11:30 na safe (GMT+1) a daidai lokacin da masu ibada a cikin cocin ke halartar Masallatai da bukukuwan Fentikos.[3][5] Wasu gungunn ‘yan bindiga ne suka shiga cocin a cikin kamannin ’yan taro, ɗauke da jakunkuna daa ke ɗauke da bindigogi. Wasu gungun ƴan bindigar sun tsayaa a wajen cocin. An tayar da wasu bama-bamai a wajen cocin inda ƙungiyoyin biyu suka fara harbe-harbe kann masu ibada.[5] Waɗanda ke wajen cocin suna ta harbi kai tsaye a cikin cocin yayin da saurann gungun yan bindigar na cikin cocin suma sukai ta harbi daga ciki, inda suka harbe wani yaro da ke sayar da alewa a kofar shiga[6][7] da masu ibadar da ke ƙoƙarin isa kofofi biyu na cocin dake buɗe. An kulle babbar hanyar shiga[8] kuma 'yan bindigar da ke ciki suna harbin duk wanda ya motsa.[9] Hotunan bidiyo naa cikin cocin sun nuna gawarwakin wadanda abin ya shafa kwance cikin jini male-male a ƙasa.[4][10] Bayan harin 'yan bindigar sun gudu cikin motaa kirar Nissan Sunny da suka sata.[5]
Wani limamin cocin da ya tsallakee rijiya da baya ya ce an kai harin ne a lokacin da cocin ke shirin rufe hidimar. Har na nemi mutane su fara tafiya, a haka ne muka fara jin karar harbe-harbe ta ɓangarori daban-daban. Mun ɓoye a cikin cocin amma wasu mutane sun fita lokacin da harin ya faru. Mun kulle kanmu a cikin coci na minti 20. Da muka ji sun tafi, sai muka buɗe coci muka garzaya da waɗanda abin ya shafa asibiti.”[11] Fr Andrew Adeniyi Abayomi ya ce ya yi ƙoƙarin karee Ikklesiya, na ci gaba da kasancewa cikin sashe na ibada. Na kasa tserewa kamar yadda yara ke kewaye da ni, wasu manya kuma suka manne da ni, wasu ma a ciki na. Na yi musu garkuwa kamar yadda kaza ke kare kajin ta.[12] “Wani limamin cocin da ya bar ginin na ɗan lokaci kafin harin ya ce yana komawa cocin ne wasu da suka tsere a waje suka tare shi suka shaida abinda ke faruwa.[13]
Wani ganau ya ce ya ga ‘yan bindiga biyar da suka kai harin.[14] An kashe ‘yan sanda biyu.[15]
Abubuwan da suka faru
gyara sasheHukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (Nigeria) NEMA ta ce a ranar 7 ga watan Yuni a kalla gawarwakin mutane 22 daga harin na cikin ɗakin ajiye gawa na asibitin yankin, ciki har da yara biyu[16] kuma akalla 58 sun samu raunuka.[17][18] Yawancin gawarwakin da aka ɗauke a cocin ‘yan uwansu ne suka kai su domin a binne, lamarin da ke nuna adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru.[16][lower-alpha 1] A ranar 9 ga Yuni gwamnati ta sake duba adadin waɗanda suka mutu zuwa akallaa 40, tana mai cewa waɗanda suka tsira da rayukansu 61 har yanzu suna asibiti.[18][20] Wani wanda aka jikkata ya mutu sakamakon raunin da ya samu daga baya.[21] An tabbatar da kashe akalla yara biyar. [22]
Shaidu da hukumomin yada labarai sun bayyana adadin mutanen da aka kashe sama da 50. Wani ɗan siyasar yankin Adelegbe Timileyin ya ce an samu asarar rayuka sama da 50 da suka haɗa da kananan yara, yayin da wasu majiyoyi suka kiyasta adadin waɗanda suka mutu ya fi yawa. [3][23] Wani likita ya ce an gano akalla gawarwaki 50. [24][25] Timileyin ya kuma ce an yi garkuwa da limamin cocin, abin da ƙungiyar Roman Katolika ta Ondo ta musanta.[14][26] Mai martaba Diocese ya fayyace cewa limamin cocin da sauran limaman cocin suna cikin koshin lafiya.[27] Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Ondo Oluwole Ogunmolasuyi ya ziyarci wurin da aka kai harin inda ya kirga a kalla mutane 20, inda ya yi kiyasin adadin waɗanda suka mutu sun kai 70 zuwa 100.[28] Likitoci sunn shaidawa manema labarai cewa harin ya janyo hasarar rayuka da dama kuma asibitocin yankin sun cika makil da waɗanda abin ya shafa.[13] kafar yaɗa labarai ta ABC News ta ambato wata majiya da ba a bayyana sunanta ba wacce ta ruwaito cewa akwai gawarwakin mutane 82 da aka ajiye a ɗakin ajiyar gawa a cikin gida yayin da wata majiya ta yi karin bayani kan ƙididdigar leken asirin Amurka na baya-bayan nan da aka yi kiyasin mutuwar sama da 80.[29]
Bayan haka
gyara sasheGwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya soke tafiyarsa a Abuja inda ya ziyarci inda aka kai harin;[30] ya bayyana harin da "mummunan abu",[31] da kuma "baƙar Lahadi a Owo".[32] Akeredolu ya sha alwashin "ba da duk abinda ake buƙata don farautar waɗannan maharan".[31] Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan kiyashin da aka yi yana mai cewa "mummunan hari ne kan masu ibada".[14] Paparoma Francis ya yi addu'a ga waɗanda abin ya shafa da "suka ji raɗaɗi a lokacin bikin".[14] Ƙungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra mai fafutukar ganin an dawo da 'yan awaren ƙabilar Igbo na ƙasar Biafra, ta kira harin a matsayin matakin da ba za a amince da shi ba, kuma harin ta'addanci ne na Musulunci, inda ta ce ya kamata kiristoci su daina dogaro da gwamnatin Najeriya wajen tabbatar da tsaron rayuwa. da kaddarorin su. . . Mulkin da ake da shi a yanzu yana da maslaha guda ɗaya kawai, ita ce maslahar Fulani.” Kungiyar IPOB ta ce ya kamata ƙungiyoyin ‘yan awaren Biafra su kare majami’u a Kudancin Najeriya.[33]
Kisan gillar ya sa matukar kaɗuwa daga zukatan al'ummar Najeriya. An soki martanin da shugaba Buhari da jam'iyyar sa ta All Progressives Congress suka mayar da cewa bai isa ba, kuma Buhari ya haifar da cece-kuce bayan da aka kama shi yana karbar bakuncin wasu 'yan jam'iyyar APC sa'o'i bayan harin.[34] Hukumar ta Amotekun ta sanar da tura dakarun ta domin kare majami'u da masallatai a jihar a ranar 12 ga watan Yuni.[35] Dattawan yankin da suka haɗa da Sarkin Owo Ajibade Gbadegesin Ogunoye III, sun yi yunƙurin kwantar da hankulan mazauna yankin bayan kisan kiyashin da aka yi domin hana kai hare-haren ramuwar gayya.[36]
Harin dai ya ɗauki hankula a duk fadin duniya, inda ƙungiyar agajin Katolika ta Aid to the Church in Need ta fitar da wata sanarwa mai dauke da cewa: ACN ta yi Allah wadai da wannan tashin hankalin, da wani harin ta'addanci da aka kai a Najeriya, daya daga cikin jerin laifuffukan da suka shafi Kiristoci. Kasar gaba daya ta yi fama da tashe-tashen hankula, ‘yan fashi da garkuwa da mutane, waɗanda duk da cewa sun shafi dukkanin ƙabilu da addinai na kasar, sun kai ga jerin manyan hare-hare kan al’ummar Kirista a cikin ‘yan shekarun da suka gabata (. . . ) ACN tana kira ga ɗaukacin shugabannin siyasa da na addini a duniya da su yi kakkausan lafazi da yin Allah wadai da wannan ta’addancin da aka kai a cocin St. Francis Xavier Catholic Church, Owo, Jihar Ondo, a kudu maso yammacin Najeriya, a lokacin bukukuwan ranar Lahadi na Fentikos.”[37]
Hukumomin Najeriya ne suka shirya jana’izar waɗanda aka kashe a ranar 17 ga watan Yuni. Yayin da ake gudanar da jana’izar, Akeredolu ya yi alkawarin inganta harkokin tsaro a jihar, ya kuma yarda cewa shi ne ya ɗauki nauyin gazawa wajen samar da tsaro.[38][39] Bishop Jude Arogundade na cocin Roman Katolika na Ondo ya soki gwamnatin Buhari da " alkawurran banza " game da tabbatar da tsaro da kuma hana ta'addanci, yana gaya wa masu halartar jana'izar cewa suna buƙatar "kwato kasar nan daga masu lalata ta."[22] Bishop Emmanuel Badejo, wanda yana ɗaya daga cikin limaman cocin da suka gudanar da jana’izar, ya bukaci gwamnati da ta “tashi, ta tashi tsaye, ta ɗauki matakin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi jama'a a faɗin Najeriya”. [38]
Alhakin kai harin
gyara sasheHar yanzu dai babu wata kungiya da ta ɗauki alhakin kai harin,[31] yayin da da yawa daga cikin 'yan ƙabilar Owo daga kabilar Yarbawa ke zargin 'yan kungiyar makiyayan Hausawa da Fulani da hada baki.[40] Ƴan sanda sun gano wasu bama-bamai guda uku da ba su tashi ba a wurin da lamarin ya faru, da kuma harsasan bindiga ƙirar AK-47 da dama.[41][42]
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ƙungiyar 'yan ta'adda ta IS-West Africa Province (ISWAP) ce ta kai harin na ranar 9 ga watan Yuni. Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ce ‘yan sanda suna bin waɗanda suka aikata laifin.[36][20] Akeredolu ya ce zargin da gwamnati ke yi ya yi gaggawar wuce gona da iri tunda ISWAP na ɗaukar alhakin kai hare-haren ta.[43][44][45]
Rundunar Amotekun a ranar 23 ga watan Yuni ta sanar da cewa ta kama wasu daga cikin waɗanda ake zargin tare da kama wasu makamai da motoci na shaida.[46] A watan Agustan shekarar 2022, rundunar sojin Najeriya ta sanar da kama wasu mutane su shida da ake zargi, sannan ta ƙara da cewa ɗaya daga cikinsu shi ne shugaban ƙungiyar ISWAP da ke shirin kai wasu hare-hare. Akeredolu ya kuma sanar da kama mutumin da ake zargi da samar da gidaje ga waɗanda ake zargin kafin a kai harin.[47]
Duba kuma
gyara sasheBayanan kula
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "Attack against Catholic church leaves 50 dead in Nigeria". DW. 5 June 2022 from DW.com. Retrieved June 18, 2022. (in Spanish)
- ↑ "Nigeria Owo church attack: Gunmen kill Catholic worshippers in Ondo". BBC News (in Turanci). 2022-06-05. Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 2022-06-05.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 "Over 50 feared dead in Nigeria church attack, officials say". AP NEWS (in Turanci). 2022-06-05. Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 2022-06-05.
- ↑ 4.0 4.1 "Nigeria: gunmen kill dozens in 'satanic' attack on Catholic church". the Guardian (in Turanci). 2022-06-05. Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 2022-06-05.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 "Owo Church Attack: Police recover 3 unexploded bombs". Vanguard News (in Turanci). 2022-06-06. Archived from the original on 7 June 2022. Retrieved 2022-06-07.
- ↑ "Nigeria church massacre: What happened and why?". www.aljazeera.com (in Turanci). Archived from the original on 6 June 2022. Retrieved 2022-06-06.
- ↑ Adetayo, Ope. "'Last prayer': Nigerian church massacre survivors recount ordeal". www.aljazeera.com (in Turanci). Archived from the original on 7 June 2022. Retrieved 2022-06-07.
- ↑ "Gunmen at Nigeria church shot from both inside and outside". AP NEWS (in Turanci). 2022-06-06. Archived from the original on 6 June 2022. Retrieved 2022-06-06.
- ↑ "Dozens feared dead after gunmen attack Nigerian church, officials say". ABC News (in Turanci). Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 2022-06-05.
- ↑ "UPDATED: Many killed in Ondo church attack". Punch Newspapers (in Turanci). 2022-06-05. Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 2022-06-05.
- ↑ "'We were locked in the church for over 20 minutes', priest speaks on Ondo attack". Daily Trust (in Turanci). 2022-06-05. Archived from the original on 6 June 2022. Retrieved 2022-06-06.
- ↑ ACN (2022-06-15). "Attack turns Pentecost Mass into bloodbath: "I shielded them as a hen shields her chicks", Nigerian priest recalls". ACN International (in Turanci). Retrieved 2022-11-18.
- ↑ 13.0 13.1 "Nigerian forces hunt for gunmen who killed 50 at church". AP NEWS (in Turanci). 2022-06-06. Archived from the original on 6 June 2022. Retrieved 2022-06-06.
- ↑ 14.0 14.1 14.2 14.3 "Worshippers gunned down during church service in Nigeria". www.aljazeera.com (in Turanci). Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 2022-06-05.
- ↑ Babajide, Abdul (2022-06-05). "Foreigners from Mali trained in Libya behind attack on Owo Catholic church – Akeredolu". Daily Post Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 2022-06-06.
- ↑ 16.0 16.1 "Infants among 22 worshippers killed in Nigeria church attack". AP NEWS (in Turanci). 2022-06-07. Archived from the original on 7 June 2022. Retrieved 2022-06-07.
- ↑ Reuters (2022-06-07). "Nigeria church attack killed 22 and injured 50, official says". Reuters (in Turanci). Archived from the original on 7 June 2022. Retrieved 2022-06-07.
- ↑ 18.0 18.1 Api, Cue (2022-06-09). "Nigeria church attack: Toll rises to 40, over 60 injured". The Hindu (in Turanci). ISSN 0971-751X. Archived from the original on 9 June 2022. Retrieved 2022-06-09.Samfuri:Subscription required
- ↑ Stephanie Busari. "Funeral mass held for victims of church gun massacre in Nigeria". CNN. Retrieved 2022-06-18.
"Some Igbo people carried their dead back to the southeast of the country. I'm still not sure how many died," she said.
- ↑ 20.0 20.1 Abuja, Reuters in (2022-06-09). "Islamic State affiliate suspected of Catholic church massacre, Nigeria says". the Guardian (in Turanci). Archived from the original on 9 June 2022. Retrieved 2022-06-09.
- ↑ "Owo massacre: Another victim dies in hospital". Punch Newspapers (in Turanci). 2022-07-14. Retrieved 2022-07-14.
- ↑ 22.0 22.1 "Nigeria funeral for church attack victims draws anger, tears". AP NEWS (in Turanci). 2022-06-17. Retrieved 2022-06-18.
- ↑ "Over 50 Feared Dead in Nigeria Church Attack, Officials say". VOA (in Turanci). Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 2022-06-05.
- ↑ Owoeye, Fikayo (2022-06-05). "At least 50 dead after gunmen attack worshippers at church in Nigeria". Reuters (in Turanci). Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 2022-06-05.
- ↑ Staff, Foreign. "Children are among dead in church attack in Nigeria". The Times (in Turanci). ISSN 0140-0460. Archived from the original on 6 June 2022. Retrieved 2022-06-05.
- ↑ "Owo attack: No priest was kidnapped, says Catholic church". Punch Newspapers (in Turanci). 2022-06-05. Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 2022-06-05.
- ↑ Owoeye, Fikayo (2022-06-05). "At least 50 killed in massacre at Catholic church in southwest Nigeria". Reuters (in Turanci). Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 2022-06-05.
- ↑ Ezeamalu, Ben; Peltier, Elian (2022-06-05). "Dozens Feared Dead in Church Attack in Nigeria". The New York Times (in Turanci). ISSN 0362-4331. Archived from the original on 6 June 2022. Retrieved 2022-06-06.
- ↑ "Over 80 feared dead in attack on Catholic church in Nigeria, sources say". ABC News. 2022-06-09. Retrieved 2022-06-13.
- ↑ "Several dead in Nigeria as gunmen attack Catholic church". The Guardian. Reuters. 5 June 2022. Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 7 June 2022.
- ↑ 31.0 31.1 31.2 "'Evil and wicked': Dozens killed in Nigeria church attack". Al Jazeera. 5 June 2022. Archived from the original on 5 June 2022. Retrieved 7 June 2022.
- ↑ Nimi Princewill and Amy Cassidy (5 June 2022). "Mass shooting at Nigeria church kills dozens, says local lawmaker". CNN. Archived from the original on 6 June 2022. Retrieved 7 June 2022.
- ↑ "IPOB declares attack on Ondo Catholic Church worshippers unacceptable". Vanguard News (in Turanci). 2022-06-08. Retrieved 2022-06-11.
- ↑ "Nigeria Owo church attack: Blood on the altar". BBC News. 6 June 2022. Archived from the original on 6 June 2022. Retrieved 7 June 2022.
- ↑ "Ondo Church Attack: Osun Deploys Amotekun Security Personnel To Protect Churches, Mosques". Sahara Reporters. 13 June 2022. Retrieved 13 June 2022.
- ↑ 36.0 36.1 Obiezu, Timothy (10 June 2022). "Nigerian Officials Say Terror Group ISWAP Behind Church Massacre". Voice of America. Retrieved 13 June 2022.
- ↑ ACN (2022-06-07). "ACN statement about the Pentecost massacre in St. Francis Xavier Church in Owo, Nigeria". ACN International (in Turanci). Retrieved 2022-11-18.
- ↑ 38.0 38.1 "Nigerian Authorities Hold Mass Burial Ceremony for Victims of Church Massacre". Voice of America. 17 June 2022. Retrieved 18 June 2022.
- ↑ Stephanie Busari. "Funeral mass held for victims of church gun massacre in Nigeria". CNN. Retrieved 2022-06-18.
- ↑ Adelaja, Temilade; Sanni, Kazeem (6 June 2022). "Pain and horror follow massacre in Nigerian Catholic church". Reuters. Archived from the original on 6 June 2022. Retrieved 7 June 2022.
- ↑ "Owo Church Attack: Police recover 3 unexploded bombs". Vanguard News. 6 June 2022. Archived from the original on 7 June 2022. Retrieved 7 June 2022.
- ↑ Adelaja, Temilade; Sanni, Kazeem (7 June 2022). "Police recover explosives following massacre in Nigerian Catholic church". Reuters. Archived from the original on 6 June 2022. Retrieved 7 June 2022.
- ↑ Adeyeye, Oluwafemi (2022-06-10). "Ondo Church Massacre: FG's conclusion on ISWAP too hasty – Akeredolu". The Witness Newspaper (in Turanci). Retrieved 2022-06-16.
- ↑ "Owo Massacre: FG's conclusion on ISWAP too hasty – Gov Akeredolu". News360 Info - Breaking News, Nigerian News and Multimedia, World News. (in Turanci). 2022-06-10. Retrieved 2022-06-16.
- ↑ Ogbuanoh, Jossey. "Ginja Me - News: Owo massacre: Federal Governments conclusion on ISWAP too hasty – Akeredolu". Ginja Me (in Turanci). Retrieved 2022-06-16.
- ↑ Leke Adegbite (23 June 2022). "Amotekun arrests suspects of Owo church attack". Radio Nigeria. Archived from the original on 26 June 2022. Retrieved 25 June 2022.
- ↑ Benedict Mayaki (12 August 2022). "Nigeria: Suspects in Owo Church attack apprehended". Vatican News. Retrieved 22 August 2022.
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Adelaja, Temilade; Sanni, Kazeem (2022-06-06). "Blood on the church walls – gruesome scenes after Nigeria attack". Reuters (in Turanci). Retrieved 2022-06-07.
- "Nigeria's Owo church massacre: Who are the victims?". BBC News (in Turanci). 2022-06-17. Retrieved 2022-06-18.