Hari a Mainok

Harin Boko Haram a arewacin Najeriya

A ranar 25 ga watan Afrilun 2021, wasu gungun ƴan ta'addar ƙungiyar ISWAP sun kashe sojoji 33 a Mainok, wani gari mai nisan mil 36 (kilomita 58) yamma da birnin Maiduguri a jihar Borno, Najeriya.[1][2]

Infotaula d'esdevenimentHari a Mainok
Iri rikici
Kwanan watan 25 ga Afirilu, 2021
Wuri Mainok (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Adadin waɗanda suka rasu 33

Harin Ta'addancin gyara sashe

Mayaƙan Sanye da kayan soji, sun iso ne a cikin manyan motoci guda huɗu masu jure wa nakiyoyi, da harbi har wayau motocin masu sulke, sai kuma manyan motocin bindiga da dama. Sun rabu gida uku kafin su kai hari sansanin sojojin. ISWAP sun lalata tankin yaki na T-55, BTR-4EN, kuma ta sace MRAPs da yawa.[3][4][5] Maharan sun tsere zuwa sansaninsu da ke kewaye da layin Lawan Mainari, yayin da sojojin saman suka kai musu farmaki ta sama.[2][6] A lokacin da ‘yan ta’addan ISWAP suka yi arangama da jiragen soji da suka nufi wajensu domin kai musu hari, a fusace suka kona ofishin ‘yan sanda da ke Mainok sannan suka tsere zuwa makarantar firamare da ke can.[7]

Lokacin da sojoji suka iso daga Damaturu don mayar da martani, ISWAP sun yi wa sojojin kwanton bauna, inda suka kashe uku, suka raunata tara, sannan suka sace MRAP.[6] Wani jirgi marar matuki ya kai harin bam da gangan kan wata motar sojoji inda ya kashe mutane 20.[8][6]

Bayan faɗan gyara sashe

An kai harin ne aka ɗauki tsawon lokaci ana gwabza faɗa a garuruwan Geidam, Kumuya da Buni Gari da ke lardin Yobe. Hukumar NAF ta tura intelligence, Surveillance and Reconnaissarce (ISR) inda aka girke su a sararin sama.[7]

Duba kuma gyara sashe

  • Lokacin rikicin Boko Haram
  • Jerin abubuwan ta'addanci a 2021

Manazarta gyara sashe

  1. "Jihadists kill 31 soldiers in northeast Nigeria". The Guardian (Nigeria). 26 April 2021. Retrieved 26 April 2021.
  2. 2.0 2.1 "More than 30 Nigerian soldiers killed in militant attack - sources". Reuters. 25 April 2021. Retrieved 25 April 2021.
  3. "CalibreObscura Backup". Telegram.
  4. "CalibreObscura Backup". Telegram.
  5. "CalibreObscura Backup". Telegram.
  6. 6.0 6.1 6.2 "How Fighter Jet, Boko Haram Killed 33 Soldiers In Mainok | Nigeria News". www.naijanews.com.
  7. 7.0 7.1 Odunsi, Wale (2021-04-25). "Nigerian military loses troops in Mainok after Boko Haram attack". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-01-27.
  8. says, Jasper (April 26, 2021). "Nigerian Air Force probes friendly fire against troops in Mainok". P.M. News.