Hama Amadou (an haife shi a shekarata 1949 kuma ya mutu Oktoba 23, 2024) dan siyasar kasar Nijar ne wanda ya rike matsayin firayiministan Nijar daga shekarar 1995 zuwa 1996 sannan kuma ya kara yi daga 2000 zuwa 2007. Ya kuma rike babban sakataren jam'iyyar su ta National Moviement for the Development of Society (MNSD-Nassara) daga 1991 zuwa 2001 da kuma shugaban jam'iyyar MNSD-Nassara na kasa baki daya daga shekarata 2001 zuwa 2009. Amadou dan kabilar Kurtey ne wani bangare na kabilun Fulani[1] kuma ya tashi ne a yankin gundumar Tillaberi kusa da tsaunukan Kogin Neja, arewa da birnin Niamey.

Hama Amadou
President of the National Assembly of Niger (en) Fassara

19 ga Afirilu, 2011 - 24 Nuwamba, 2014
firaministan Jamhuriyar Nijar

1 ga Janairu, 2000 - 7 ga Yuni, 2007
Ibrahim Hassane Mayaki - Seyni Oumarou
firaministan Jamhuriyar Nijar

21 ga Faburairu, 1995 - 27 ga Janairu, 1996
Amadou Cissé - Boukary Adji
Member of the National Assembly of Niger (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Youri, 1950
ƙasa Nijar
Ƙabila Mutanen Fulani
Mutuwa Niamey, 23 Oktoba 2024
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa National Movement for the Development of Society (en) Fassara
Hama Amadou

A sakamakon badakalar cin hanci da rashawa a gwamnatinsa, aka cire shi daga ofishin sa na matsayin firayiminista. A shekarata 2008 ne aka saka shi a layin wanda za'a kama domin yi masa bincike daya shafi aikata muggan laifuka a babbar kotun taraiyar Nijar, tare da kuma cire shi daga matsayin sa na Shiva ban jam'iyyar MNSD.

Daga shekarar 2011 zuwa shekarata 2014, Amadou shine shugaban majalisar dokokin Nijar. Ya bar kasar shi ta Nijar a shekarata 2014 domin ya gudanar ma kamun da hukuma ke son yi masa bisa ga zargin da hukumar tayi masa na safarar jarirai daga Najeriya. Sakamakon wannan zargin ne kotu ta yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na shekara tara a 2017.[2] Amadou yayi gudun hijira zuwa Kaspar Faransa.[3]

Hama Amadou tare da ambassada Williams

Manazarta

gyara sashe
  1. In French: Peul; in Fula: Fulɓe.
  2. AfricaNews (2017-03-14). "Niger opposition leader sentenced to one year in prison for alleged baby trafficking". Africanews. Retrieved 2017-03-14.
  3. "Niger's opposition leader Hama Amadou jailed in absentia". BBC News (in Turanci). 2017-03-13. Retrieved 2017-03-15.