Hajiya Hafsat Abdullahi Ganduje (wadda aka fi sani da Gwaggo) 'yar Najeriya ce, farfesa, Masaniyar Harkar Siyasa a Najeriya kuma matar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ce, sannan kuma memba ce a jam'iyyar All Progressive Congress.[1]

Hafsat Ganduje
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano, 28 Disamba 1960 (63 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Abdullahi Umar Ganduje
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a Malami
Hajia hafsat ganduje
Hajia hafsah da mijin ta ganduje

Tarihin Rayuwa da Karatu

gyara sashe

An haifi Hafsat Ganduje a jihar Kano.Ta halarci makarantar firamare ta Malam Madori, da makarantar firamare ta kwana a jihar Kano, da Kwalejin Mata ta garin Kano. Hafsat Ganduje ta samu digiri na farko na fannin Kimiyyan Ilimi, acikin shekara ta dubu daya da Dari Tara da tamanin da daya (1981), ta zama Jagoran Ilimin halin ɗan Adam, a shekara ta alif ɗari tara da chasain da biyu (1992), ta zama Jagora na Kasuwanci, a shekara ta dubu biyu da hudu (2004), ta zama Doctor na fannin Falsafa a cikin Gudanarwa da Tsare-tsare, a shekara ta dubu biyu da Sha biyar(2015) duk daga Jami'ar Bayero, Kano.[2]

Ganduje ta fara aiki ne a matsayin malama a aji sannan bayan ta zama shugabar makaranta, daga baya ta zama malama a Kwalejin Ilimi ta Jami'ar Bayero, Kano, Najeriya. Jami'ar Maryniam Abacha ta Nijar ce ta ɗaga darajar ta zuwa matsayin Farfesa a shekara ta (2019).

Ita abokiyar zama memba ce a Cibiyar Gudanarwa ta ƙasar Nijeriya kuma ta samu lambobin yabo da yawa.

Aure da Iyali

gyara sashe

Hafsat, ta auri Alhaji Abdullahi Umar Ganduje wanda a yanzu haka shi ne gwamnan Jihar Kano, sannan Allah ya albarkace su da ‘ya’ya.

Duk da cewa Hafsat ba ta da ofis ɗin amatsayin matar gwamna da ake kira ‘First Lady’, amma ta himmatu a ƙashin kanta wajen fito da shirye-shirye da tsare-tsaren da suke samar wa mata ayyukan dogaro da kai, gangamin samar da tallafin kayan karatu, kekunan ɗinki, tallafin kuɗaɗe domin mata su fara gudanar da ‘yan kananan sana’o’in dogaro da kai agarin Kano, dubban ɗaruruwan mata ne suka amfana da ƙoƙarinta da azamarta wacce suke ƙiran hakan a matsayin jinƙai a gare su.[3]

Farfaganda

gyara sashe

An yi ta yaɗa jita-jitan cewa Hafsat tana kaka-gida cikin sha’anin mulkin mijinta wanda ake cewa tana bayyana ra’ayinta ko lamunce ma waɗanda take son a basu kwangila ko naɗin mukamai, amma jami’an gwamnatin jihar sun sha karta wannan batun da cewa ba ta katsalandan wa gwamnan a sha’anin tafiyar da mulkin jihar Kano.

Manazarta

gyara sashe

 

  1. https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/484916-after-shunning-efcc-invitation-gandujes-wife-attends-sons-graduation-in-london.html?tztc=1
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-07. Retrieved 2023-07-07.
  3. https://www.rfi.fr/ha/najeriya/20211005-jami-an-efcc-sun-kame-matar-gwamnan-kano-hafsat-ganduje