Gundumar Sanatan Benuwai ta Kudu

majalisar dattawa a Najeriya

Gundumar Sanatan Benuwai ta Kudu ta haɗa ƙananan hukumomin Ado, Agatu, Apa, Obi, Ogbadibo, Ohimini, Oju, Okpokwu, Otukpo da Gboko[1] Akwai ƴan shugabannin majalisar dattijai guda biyu da suka fito daga gundumar, Ameh Ebute wanda ya kasance shugaban Majalisa a jamhuriya ta uku kuma shugaba mafi karancin shekaru, da kuma David Mark, shugaban majalisar dattawan Najeriya mafi dadewa. Ita ce gundumar ɗaya tilo da ta haɗa shugabannin majalisar dattawa guda biyu inda jihar Benue ta kasance jiha daya tilo da ta samu shugabannin majalisar dattawa uku tare da Iyorchia Ayu daga Benue Arewa-maso-Yamma kuma a matsayin shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta uku. An fara zaɓen David Mark a shekarar 1999 kuma ya sauka a ƙarshen wa’adinsa na 5 a Majalisar Dattawa a shekarar 2019 (bayan ya shafe shekaru 20 yana majalisar).[2][3] A halin yanzu Sanatan dake wakiltar Benue ta Kudu shine Abba Moro na jam'iyyar PDP.[4][5]

Benue South
senatorial district of Nigeria (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaBenue

Jerin Sanatocin da suka wakilci gundumar

gyara sashe
Sanata Jam'iyya Shekarar Majalisa ta
Ameh Ebute SDP 5 ga watan Disamba 1992 – 17 Nuwamba 1993 (shugaban majalisa) 3
David Mark PDP 3 Yuni 1999 – 9 Yuni 2019 4, 5, 6, (shugaban majalisa), 7 (shugaban majalisa), 8
Abba Moro PDP 11 Yuni 2019 – zuwa yanzu 9 da 10

Manazarta

gyara sashe
  1. "'Electoral body, security agencies conspired to scuttle Benue South peoples' wish'". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2019-02-25. Retrieved 2020-05-16.
  2. "High expectations as Benue South elects another senator after Mark's 20-year representation". Punch Newspapers (in Turanci). 5 February 2019. Retrieved 2020-05-16.
  3. editor (2019-05-06). "Mark Begins Thank You Tour of Benue South after Spending 20 Years in Senate". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2020-05-16.CS1 maint: extra text: authors list (link)
  4. Staff, Daily Post (2019-06-12). "Abba Moro replaces Senator David Mark in Benue South after 20 years". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2020-05-16.
  5. Emmanuel, Hope Abah; Makurdi (2019-02-26). "Abba Moro wins Benue South Senate seat". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2020-05-16.