Jihar Gongola tsohuwar jiha ce a Najeriya. An kirkiro ta ne a ranar 3 ga Fabrairu 1976 daga Lardunan Adamawa da Sardauna na Jihar Arewa, tare da Rukuni na Wukari na Jihar Benuwai da Filato na wancan lokacin; jihar ta wanzu har zuwa 27 ga Agusta 1991, lokacin da aka raba ta zuwa jihohi biyu, Adamawa da Taraba. Garin Yola shi ne babban birnin jihar Gongola.

Jihar Gongola


Wuri
Map
 8°30′N 11°45′E / 8.5°N 11.75°E / 8.5; 11.75

Babban birni Yola
Bayanan tarihi
Mabiyi Jihar Arewa maso Gabas da Jihar Benue-Plateau
Ƙirƙira 3 ga Faburairu, 1976
Rushewa 27 ga Augusta, 1991
Ta biyo baya Jihar Adamawa da Taraba state
Taswirar jihar Gongola.

Majalisar zartarwa ce ke mulkin jihar Gongola.

Manazarta gyara sashe