Gbenga Ogedegbe
Gbenga Ogedegbe wani likitan Amurka ne dan Najeriya wanda manufarsa ita ce "kawo kiwon lafiya a cikin unguwanni daban-daban na birnin New York don biyan bukatun kiwon lafiya na musamman".[1] Shi Farfesa ne a fannin Kiwon Lafiyar Jama'a da Magunguna a Jami'ar New York kuma yana rike da wasu mukaman likitanci a kasar.[2]
Farkon rayuwa da ilimi
gyara sasheAn haifi Ogedegbe a Legas. Ya halarci Hussey College, Warri. Ya yanke shawarar cewa yana son zama likita yana dan shekara takwas.[1] Bayan ya kammala karatunsa na sakandare, ya yi karatun likitanci a jami'ar Donetsk ta kasar Ukraniya. Ba da dadewa ba bayan ya kammala karatun likitanci ya koma Amurka, inda ya kansance dalibin likitanci a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Montefiore.[2] Daga baya ya shiga Jami'ar Columbia, inda ya kammala digiri na biyu a fannin lafiyar jama'a. Ya gudanar da hadin gwiwar bincike a duka Kwalejin Magunguna ta Weill Cornell da Kwalejin Magunguna ta Albert Einstein.[2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Dr. Gbenga Ogedegbe: Physician-Scientist, Barbershop Regular". NYU Langone. Archived from the original on 2021-01-21. Retrieved 2023-06-17.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 "Dr. Gbenga Ogedegbe Biography". All American Speakers Bureau. Archived from the original on 2023-03-12. Retrieved 2023-06-17.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)