Garkuwa Da mutane A Kagara
A ranar 17 ga watan Fabrairu, 2021, wasu mahara dauke da makamai suka kashe wani dalibin makaranta sannan wasu mutane 27 suka sace su da misalin karfe 3 na safe daga makarantarsu da ke Kagara, Jihar Neja, a Najeriya . An kuma yi awon gaba da wasu ma’aikatan makarantar uku da danginsu 12. Babu wanda ya dauki alhakin harin.
Iri |
aukuwa Garkuwa da Mutane |
---|---|
Kwanan watan | 17 ga Faburairu, 2021 |
Wuri | Masarautar Kagara |
Ƙasa | Najeriya |
Nufi | makaranta |
Adadin waɗanda suka rasu | 1 |
Kai hari
gyara sashe‘Yan bindigar sun kai samame ne a kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke gundumar Kagara a jihar Neja da misalin karfe biyu na dare.
Amsar gwamnati
gyara sasheShugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya umarci ‘yan sanda da sojoji su gudanar da aikin ceto.
Yayin da ake ci gaba da bincike, wani jami’in tsaro da ba a bayyana sunansa ba ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Faransa cewa ana kyautata zaton maharan ‘yan kungiyar asiri ne.
A ranar 19 ga watan Fabrairu, shekara ta 2021 gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani-Bello, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na kan matakin karshe na tattaunawa da 'yan ta'addan game da sakin mutanen.
A ranar 21 ga watan Fabrairu, shekara ta 2021, wani jirgin saman soja yana kan hanyarsa ta zuwa Minna don kokarin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su. Daga nan jirgin ya fado, ya kashe duka mutane 7 da ke cikinsa. Shugaban hafsan sojan sama ya ba da umarnin gudanar da bincike nan take, don fayyace idan hatsarin na bazata ne ko a'a.
A ranar 24 ga Fabrairu, kafofin yada labarai sun ruwaito cewa masu satar mutanen suna tattaunawa da iyayen ’yan matan makarantar da aka sace don biyan kudin fansa don sake su. Wani wakilin iyayen ya yi tayin biyan fansar fam miliyan ₦ 2.7. Jagoran masu garkuwar wanda aka bayyana a kafafen yada labarai mai suna Dogo Gide, ya bukaci lambar wayar iyayen ne domin ya tattauna da kowannensu kai tsaye. Gwamnatin jihar Neja ta dage kan cewa har yanzu tana cikin tattaunawa da masu satar mutanen don sakin wadanda aka sace ba tare da wani sharadi ba.
Saki
gyara sasheA ranar 27 ga Fabrairu 2021, gwamnatin jihar Neja ta ba da sanarwar cewa dukkan mutane 42 da aka sace daga makarantar Kagara ’yan bindiga sun sake su kuma gwamnatin jihar Neja ta karbe su.
Duba kuma
gyara sashe- Satar Zamfara