Garba Lawal

Dan Wasan kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya

Garba Lawal (an haife shi a ranar 22 ga watan Mayun shekarata alif 1974) ya kassnce tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Nijeriya wanda ya taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya na hagu. A shekara ta ( 2014) ya zama babban manaja a Kaduna United FC

Garba Lawal
Rayuwa
Haihuwa Jahar Kaduna, 22 Mayu 1974 (50 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football manager (en) Fassara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya1993-2006535
Bridge F.C. (en) Fassara1993-1995
Espérance Sportive de Tunis (en) Fassara1995-1996
  Roda JC Kerkrade (en) Fassara1996-200215420
  PFC Levski Sofia (en) Fassara2002-2003153
  PFC Levski Sofia (en) Fassara2002-2003
IF Elfsborg (en) Fassara2004-2004120
C.D. Santa Clara (en) Fassara2004-2005160
G.S. Iraklis Thessalonikis (men's association football) (en) Fassara2005-2006331
Bridge F.C. (en) Fassara2007-2007188
Guangzhou City F.C. (en) Fassara2007-200730
Lobi Stars F.C. (en) Fassara2009-201231
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Nauyi 72 kg
Tsayi 183 cm

A matsayin dan wasa, Lawal ya kasance mafi nasara a lokacinsa a Roda JC a cikin Eredivisie . Ya kuma buga wa kulob din Julius Berger FC a Najeriya da Changsha Ginde ta China.

Mataki na Duniya

gyara sashe

Ana daukar Lawal a matsayin daya daga cikin fitattun 'yan wasa a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ta shekara ta 1990), da farkon (2000), galibi ana amfani da shi ga kowane matsayi daga tsaro zuwa kai hari a bangaren hagu. Lawal ya halarci gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekara ta (1998), inda ya taka rawangani a wasan da suka doke Spain da ci 3-2 a wasan farko da Najeriya ta buga a gasar, da kuma a shekara ta ( 2002), Ya lashe lambar zinari na Olympics a shekara ta (1996), Ya wakilci Najeriya a wasanni hudu na Kofin Kasashen Afirka : (2000, 2002, 2004 da 2006), inda ya ci duka amma ban da na farko.

Horar da 'Yan Wasa

gyara sashe

A watan Agustan shekara ta ( 2009), an nada Lawal a matsayin mataimakin kocin Lobi Stars FC A cikin wannan shekarar, aka dauke shi aiki a matsayin mai kula da kungiyar kwallon kafa ta kasa na 'ysn ƙasa da shekaru 17.

Lambobin Yabo

gyara sashe

Roda JC

  • Kofin KNVB :( 1996 zuwa 1997 da 1999 zuwa 2000)

Levski Sofia

  • Kofin Bulgaria :( 2002 zuwa 2003)

Manazarta

gyara sashe