Adefunmilayo Tejuosho (née Smith) (an haife ta a ranar ashirin da biyar 25 ga Maris, shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da dari biyar 1965) ‘yar siyasan Nijeriya ce wacce ke wa’adin ta na hudu matsayin 'yar majalisar[1] dokokin Jihar Legas, tana wakiltar Mazabar Mushin I. Ita ce shugabar kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Legas a kan Kudade. Tayi aure inda take da yara hudu ita da mijinta.

Funmi Tejuosho
Rayuwa
Haihuwa jahar Lagos, 25 ga Maris, 1965 (59 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta University of Buckingham (en) Fassara Digiri a kimiyya
West Virginia University (en) Fassara
Jami'ar jahar Lagos Doctor of Philosophy (en) Fassara
Sana'a
Sana'a masana da ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Farkon Rayuwa da Karatu

gyara sashe

An haifi Tejuosho ne a jihar Legas ga iyalin Ademola Smith[2] masanin cututtuka wanda ke yi wa gwamnatin Najeriya aiki. Ta halarci Makarantar University of Lagos Staff School, Akoka, Queen's College, Lagos sannan ta kammala karatun sakandare a West Virginia.[3] Bayan ta kammala karatun ta na sakandare ne, ta halarci jami’ar West Virginia inda ta karanci Biology.[3] Daga baya ta sami digiri a fannin Law daga Jami'ar Buckingham.[4] Tejuosho ta sami digirin digirgir a Law daga Jami'ar Legas.[5]

Aiki da Siyasa

gyara sashe

A lokacin aikinta na bautar kasa, ta kasance malama a makarantar sakandarenta, Queens School, Yaba. Bayan ta zama kwararran lauya, ta shiga aikin Ademola Odunsi & Co. A shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da shida 1996, ta kasance mamba na Grassroot Democratic Movement a karkashin gajeriyar gwamnatin Abacha kuma ta kasance 'yar takarar 'yar majalisar wakilai na jam'iyyar kafin aikin rushewar dimokiradiyya. A farkon jamhuriya ta huɗu, ta shiga Alliance for Democracy.

A shekarar alif dubu biyu da ukku 2003, an zabe ta a Majalisar Dokokin Jihar Legas don wakiltar Mazabar Mushin ta I. A cikin majalisar, Tejuosho ta dauki nauyin wani doka wanda daga baya akafi sani da Dokar Kare Hakkin Rikicin Cikin Gida ta Jihar Legas wato (Lagos State Protection Against Domestic Violence Law ta shekarar alif dubu biyu da bakwai 2007). Doka ta ba da umarnin kariya ga wadanda aka cutar daga wadanda suke cutar da su. Ta yi alfaharin rubuta daftarin dokar ta hanyar wata takarda kan rikicin cikin gida da ta rubuta don binciken ta na LLM a Jami'ar Legas.[6]

Ta ci gaba da rike mukamai da daban-daban a majalisar da suka hada da Mataimakiyar Cif Whip, Mataimakiyar Shugaban Majalisar da Chairman, Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Legas kan harkokin Kudi.[7][8][9]

Mataimakiya

gyara sashe

An zabe ta a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar a 2007 amma an tsige ta a shekarar 2009. Biyo bayan tsige ta an gudanar da wasu bincike don tabbatar da cancantar ilimin magajin na ta da kuma wasu daga masu zargin ta amma ba a fitar da sakamakon zargin ba.[10]

Rayuwar mutum

gyara sashe

Tana auren Omoba Kayode Tejuosho na gidan sarautar Tejuosho na jihar Ogun, Najeriya.[5] Suna da 'ya'ya huɗu tare.[11]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2019-07-02. Retrieved 2020-11-09.
  2. "Oladesu, Emmanuel (May 12, 2014). "Who is next Lagos deputy governor". The Nation. Lagos.
  3. 3.0 3.1 "Adesanya, Lanre (May 6, 2013). "The True Lagos Legislator – Hon. Funmilayo Tejuoso". National Daily. Lagos.
  4. "My Husband Supports Every Move I Make – Funmi Tejuoso, Lagos Assembly Best Dressed Female Lawmaker". The Gazelle News. 26 August 2013. Retrieved 16 July 2016.
  5. 5.0 5.1 "HON. FUNMI TEJUOSO LOSES FATHER". Ecomium Magazine. 19 February 2014. Retrieved 16 July 2016.
  6. "Odueme, Stella (April 21, 2010). "Legislating Against Domestic Violence". Daily Independent. Lagos.
  7. "Akinola, Wale (3 May 2015). "Why I want to be Lagos House Speaker, by Hon. Funmi Tejuosho". Vanguard News. Retrieved 16 July 2016.
  8. "Experienced Funmi Tejuoso Joins Lagos Speakership Race; Says I'm Most Qualified For The Job". The Gazelle News. 26 April 2015. Retrieved 16 July2016.
  9. 'Ezeamalu, Ben (7 June 2015). "Groups back Tejuosho to become first female Speaker in Lagos". Premium Times. Retrieved 16 July 2016.
  10. "Aka, Olabode (2012). Nigerian women of distinction, honour and exemplary presidential qualities. p. 91-93.
  11. "Hon. Funmi Tejuosho enumerates what life has taught her at 49". Ecomium Magazine. 28 March 2014. Retrieved 16 July 2016.