Francisca Onaolapo Oladipo (an haife ta a ranar 15 ga watan Janairu 1978). Farfesa ce 'yar Najeriya a fannin Kimiyyar Kwamfuta, shugaba kuma marubuciya. Tun daga shekarar 2022, ita ce Mataimakiyar Shugaban Jami'ar Thomas Adewumi, Najeriya.[1][2] Kafin naɗin nata, ta kasance Daraktar tabbatar da inganci a Jami'ar Tarayya, Lokoja, Jihar Kogi, Najeriya. Ita ce Babbar Jami'ar Gudanarwa, Virus Outbreak Data Network Africa da Asiya (VODANA).[3][2] Ita ce mace ta farko da ta zama mamba a majalisar gudanarwa a jami'ar tarayya dake Lokoja, sannan kuma mace ta farko shugabar sashin ilimin na'ura mai kwakwalwa a jami'ar.[2][4]

Francisca Oladipo
Rayuwa
Haihuwa Idanre, 15 ga Janairu, 1978 (46 shekaru)
Sana'a
Sana'a Furogirama da computer scientist (en) Fassara

A shekarar 2010, Oladipo ta samu digirin digirgir a fannin kimiyyar kwamfuta a Jami’ar Nnamdi Azikiwe dake Najeriya.[5] Ta samu Digiri na biyu da Digiri na farko a Jami’a guda. A cikin shekarar 2014, ta kasance abokiyar karatun digiri a Cibiyar Fasaha ta Massachusetts a ƙarƙashin TOTAL-MIT Karfafawa da Ƙaddamar da Malamai.[6][7]

Ta ɓullo da Python Programming Language a cikin Shirin Ilimin Kimiyyar Kwamfuta a Jami'ar Tarayya, Lokoja kuma ta kafa kungiyar PyFUL don haɓaka koyon Programming Language.[8] Ta raba aikinta a PyCon,[9] kuma wasu sun ambaci aikinta akan Python.[10] Oladipo ta kasance mai ba da shawara ga buƙatun buɗaɗɗun bayanai yayin bala'in cutar COVID-19,[11] batun da ta gabatar a cikin wallafe-wallafen[12] da ake bitar su kuma a matsayinta na mai ba da shawara a Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Amurka ta shekarar 2021 na Annobar cutar COVID-19 da Big Data.[13]

Kyaututtuka da karramawa

gyara sashe

Oladipo ta kasance Masaniya (Faculty Scholar) a Kwalejin Grace Hopper, kuma a cikin shekarar 2016 an karrama aikinta na koya wa 'yan mata matasa game da lafiyar haihuwa ta hanyar aikace-aikacen wayar hannu na ilimi (Educational Mobile Application).[14] A cikin shekarar 2020, Oladipo tana ɗaya daga cikin mutane 18 da aka ambata a matsayin ƙwararrun ƴan ƙungiyar Kwamfuta ta Najeriya.[15]

Zaɓaɓɓun wallafe-wallafe

gyara sashe
  • Awoleye, Michael Olusesan; Siyanbola, Willie Owolabi; Oladipupo, Onaolapo Francisca (20 April 2008). "Adoption Assessment of Internet Usage Amongst Undergraduates In Nigeria Universities -A Case Study Approach". Journal of Technology Management & Innovation. 3 (1): 84–89. ISSN 0718-2724.

Manazarta

gyara sashe
  1. Campus Connect. "Professor Francisca Oladipo Appointed as the Pioneer Director of Quality Assurance, FUL". campusconnect.com.ng. Retrieved April 8, 2020.[permanent dead link]
  2. 2.0 2.1 2.2 "VODANA Executive Secretary, Prof Francisca Oladipo appointed as the Pioneer Director of Quality Assurance, Federal University Lokoja, Nigeria". www.vodan-totafrica.info (in Turanci). VODAN Africa & Asia. Retrieved 2022-01-15.
  3. Campus Connect. "Professor Francisca Oladipo Appointed as the Pioneer Director of Quality Assurance, FUL". campusconnect.com.ng. Retrieved April 8, 2020.[permanent dead link]
  4. fulokoja. "Francisca Onaolapo Oladipo". fulokoja.edu.ng. Retrieved March 26, 2020.
  5. "Oladipo". Africa Scientists Directory. Retrieved 8 April 2021.
  6. Jessica Fjimori. "A new leadership cadre for science and engineering". MIT News. Retrieved April 8, 2020.
  7. Oredola, Tayo (2017-02-08). "Total, MIT, others task NUC on human capacity building". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Retrieved 2022-03-05.[permanent dead link]
  8. PyCon Clevaland 2019. "Francisca Onaolapo Oladipo". us.pycon.org. Retrieved April 8, 2020.
  9. "Presentation: Implementing a Chatbot for Positive Reinforcement in Young Learners | PyCon 2019 in Cleveland, Ohio". us.pycon.org. Retrieved 2022-01-15.
  10. Agbo, Friday Joseph; Oyelere, Solomon Sunday; Suhonen, Jarkko; Laine, Teemu H. (2021-09-01). "Co-design of mini games for learning computational thinking in an online environment". Education and Information Technologies (in Turanci). 26 (5): 5815–5849. doi:10.1007/s10639-021-10515-1. ISSN 1573-7608. PMC 8097249 Check |pmc= value (help). PMID 33967590 Check |pmid= value (help).
  11. "Contribution to the panel discussions at the First Session of the Intergovernmental Preparatory Committee for LDC5" (PDF). United Nations. May 20, 2021. Retrieved January 15, 2022.
  12. Reisen, Mirjam; Oladipo, Francisca; Stokmans, Mia; Mpezamihgo, Mouhamed; Folorunso, Sakinat; Schultes, Erik; Basajja, Mariam; Aktau, Aliya; Amare, Samson Yohannes; Taye, Getu Tadele; Purnama Jati, Putu Hadi (2021). "Design of a FAIR digital data health infrastructure in Africa for COVID‐19 reporting and research". Advanced Genetics (in Turanci). 2 (2): e10050. doi:10.1002/ggn2.10050. ISSN 2641-6573. PMC 8420285 Check |pmc= value (help). PMID 34514430 Check |pmid= value (help).
  13. "Data-Informed Societies Achieving Sustainability: Tasks for the Global Scientific, Engineering, and Medical Communities: A Virtual Workshop". www.nationalacademies.org. September 2021. Retrieved 2022-01-15.
  14. Tech Women (25 October 2016). "GRACE HOPPER CELEBRATION UNITES FELLOWS AND MENTORS IN HOUSTON". techwomen.org. Retrieved April 8, 2020.
  15. "ANNUAL GENERAL REPORTS 2020" (PDF).