Femi Ojo Ade
Femi Ojo Ade (An haifeshi ranar 23 ga watan Yuli, 1941 - 19 ga watan Mayu, 2019 [1]) marubucin Najeriya ne, mawaƙi, mai suka game da batutuwa, kuma Farfesa Emeritus na Nazarin Faransanci da Tarihin Baƙar fata.[2][3]
Femi Ojo Ade | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Lagos,, 23 ga Yuli, 1941 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | 19 Mayu 2019 |
Karatu | |
Makaranta |
Queen's University (en) University of Toronto (en) McMaster University (en) |
Harsuna |
Faransanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | literary critic (en) , maiwaƙe da Malami |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Femi ne a birnin Lagos dake kudu maso yammacin Najeriya. [4] Ya yi karatun firamare a Model Primary School da ke Yaba, Jihar Legas, sannan ya yi sakandare a Kwalejin Gwamnati da ke Ibadan, inda ya samu shaidar kammala sakandare a shekarar 1961.[5] Daga baya ya wuce Jami'ar McMaster, inda ya sami digiri na farko a fannin Arts a sashen Faransanci da Mutanen Espanya a 1967, da digiri na biyu: Master of Arts a fannin Faransanci a Jami'ar Sarauniya a shekarar 1969.[6] A shekara ta 1975, ya sami digirin digir-gir (Ph.D) a Faransanci a Jami'ar Toronto.[7] A 1975, ya shiga hidimar Kwalejin Barber–Scotia inda ya yi karatu a takaice kafin ya koma Jami’ar Obafemi Awolowo inda aka naɗa shi Farfesa a harshen Faransanci a 1980.[8] Ya yi aiki a cibiyoyin ilimi da dama tare da ba da gudummawa ga baƙar fata da al'adu.[9]
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://femi-ojoade.muchloved.com/ [dead link]
- ↑ "Ojo-Ade, Ezeigbo make case for quality poetry". The Punch. Archived from the original on 28 February 2015. Retrieved 25 February 2015.
- ↑ Ojo-Ade, Femi (1999). Ken Saro-Wiwa. Africana Legacy Press, Incorporated. ISBN 9780966383713. Retrieved 25 February 2015 – via google.nl.
- ↑ "Diaspora Wazobia Magazine - Celebrating Achievements of Nigerians in Diaspora – Femi Ojo-Ade". diasporawazobia.com. Archived from the original on 26 February 2015. Retrieved 25 February 2015.
- ↑ "Nigeria: I Cherish Most African Novels on Culture - Ojo-Ade", Daily Independent (Lagos), 5 February 2011.
- ↑ Albert S. Gérard, ed. (1986). European-language Writing in Sub-Saharan Africa. John Benjamins. ISBN 9630538326. Retrieved 25 February 2015.
- ↑ "Ojo-Ade returns in French and English colours". The Punch. Archived from the original on 28 February 2015. Retrieved 25 February 2015.
- ↑ Femi Ojo-Ade (2010). Aime Cesaire's African Theatre: Of Poets, Prophets and Politicians. ISBN 9781592217397.
- ↑ "African Books Collective". africanbookscollective.com. Retrieved 25 February 2015.