Felix A. Obuah

Ɗan siyasar Najeriya

Felix Amaechi Obuah (an haife shi ranar 16 ga watan Disamba[yaushe?]) ɗan kasuwan Najeriya ne, ɗan siyasa kuma ɗan agaji wanda ya fito daga Omoku, Jihar Ribas, Najeriya. Ya kasance shugaban jam’iyyar People’s Democratic Party na jihar Ribas tun daga shekarar 2013, kuma an sake zaɓen shi a watan Mayun 2016 a karo na biyu. Obuah yana da digiri na farko a fannin kasuwanci daga Jami'ar Ibadan.

Felix A. Obuah
Rayuwa
Haihuwa Omoku
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da ɗan kasuwa
Imani
Jam'iyar siyasa Rivers State People's Democratic Party (en) Fassara

Obuah ya taɓa zama shugaban kansila na karamar hukumar Ogba–Egbema – Ndoni a jihar Ribas. Ya kuma taɓa zama shugaban ƙungiyar masu mallakar gidaje ta Najeriya (OMPALAN) na ƙasa.[1][2][3] Obuah dai ya kasance ɗan takara ne na zaɓen shekarar 2015 , yayin da ya nuna jajircewa wajen tabbatar da zaɓen Ezenwo Nyesom Wike.

A watan Yunin 2015, an naɗa shi Shugaban Hukumar Kula da Sharar shara ta Jihar Ribas.[4]

Rayuwa ta sirri gyara sashe

Mahaifinsa Bethel Chukujindu Obuah, Kirista ne mai ibada, ya rasu yana da shekara 85 a shekara ta 2016.[5]

Duba kuma gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. "Our Team". Fezinat Group. Retrieved 5 November 2014.
  2. Onoyume, Jimitota (19 April 2013). "New Rivers pdp chair resumes at party secretariat". Vanguard. Retrieved 5 November 2014.
  3. "Rivers PDP Chairman, Bro Obuah, Congratulates Gov Faose On Inauguration". National Network. Retrieved 5 November 2014.[permanent dead link]
  4. "Refuse Contractors, Others Jitter As Obuah Takes over RIWAMA". National Network. 13 June 2015. Archived from the original on 22 June 2015. Retrieved 22 June 2015.
  5. "Banigo Extols Pa Obuah". The Tide. Port Harcourt. 5 August 2015. Retrieved 11 August 2016.