Omoku

Birni a Ogba/Egbema/Ndoni, Jihar Ribas, Nijeriya

Omoku gari ne, da ke a Jihar Ribas, a Najeriya, mai yawan jama'a kusan dubu 200,000. Birnin na a yankin Arewacin jihar, kusa da kan iyakar Jihohin; jihar Delta da jihar Imo. Hedikwatar karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni ce kuma ɗaya daga cikin manyan biranen mutanen Ogba da jihar Ribas ta Najeriya. Ita ce kuma babban birnin ƙasar Oba na Ogba. ’Yan asalin yankin suna magana da yaren Ogba na dangin harshen Igboid.

Omoku

Wuri
Map
 5°20′31″N 6°39′22″E / 5.342°N 6.656°E / 5.342; 6.656
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar rivers
Ƙaramar hukuma a NijeriyaOgba–Egbema–Ndoni
Labarin ƙasa
Yawan fili 52 km²

Kamfanonin mai da ke aiki a wurin sun haɗa da Shell Development Petroleum, Total Exploration & Production Nigeria da kuma Nigerian Agip Oil Company. An inganta ababen more rayuwa na birnin tare da gina hanyoyin mota biyu, tashar samar da wutar lantarki da kuma bankuna.

Omoku yana jin daɗin ingantaccen wutar lantarki. Amma a baya-bayan nan,  Kamfanonin mai da ke samar da wadannan ayyuka kyauta suna fuskantar ƙalubale sosai wajen samar da wannan aiki. Wannan ƙila ba za a haɗa shi da saurin girma da ci gaban da ba a kula ba akan wannan aiki na zamantakew a Najeriya.[ana buƙatar hujja]

Wasanni gyara sashe

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Go Round F.C. tana buga gasar firimiya ta Najeriya tun shekarar 2018. Ƙungiyar ƙwallon ƙafar na a garin Omoku, jihar Rivers, Nijeriya. Suna buga wasansu na gida a filin wasa na, Krisdera Hotel Stadium. A yanzu haka suna taka leda a wasan na biyu na gasar kwallon kafa ta Najeriya. Kulob din mallakar Felix A. Obuah ne kuma Ngozi Elechi ce ke jagorantar kungiyar.[ana buƙatar hujja]

Fitattun Mutane gyara sashe

Manazarta gyara sashe

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe