Farida Jalal (An haife ta ranar 2 ga watan Nuwambar, shekara ta alif ɗari tara da tamanin da biyar 1985) na Miladiyya. A birnin Katsina. Ƴar wasan fim ce a masana'antar fina-finan Arewacin kasar Najeriya da aka fi sani da Kannywood.[1]

Farida Jalal
Rayuwa
Haihuwa Jihar Katsina, 2 Nuwamba, 1985 (38 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Karatu
Harsuna Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan wasan kwaikwayo, Jarumi, gospel singer (en) Fassara da ɗan kasuwa

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Farida Jallal ne a ranar 2 ga watan Nuwamba, shekarar 1985 a birnin Katsina, Jihar Katsina. Farida ta taso ne kuma ta yi karatu a jiharta ta Katsina inda daga baya ta koma jihar Kano ta fara sana’ar fim a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.[2]

Farida ta shiga harkar fim ne a shekarar 2002 inda ta fito a manyan fina-finan masana’antu na lokacin kamar Yakana, Sansani da Madadi. An dakatar da Jaruma Farida Jallal daga yin fim na wasu lokuta saboda hana wasu jaruman fina-finai da gwamnatin jihar Kano ta yi.[3] A Shekarar 2019, Farida har ta sake fitowa a Kannywood.[4] A lokacin ta bayyana cewa ta dawo harkar fim har ma ta sanar da cewa nan ba da daɗewa ba za ta fitar da fina-finanta. A wata hira da ta yi da BBC Hausa, Farida ta bayyana cewa har yanzu ana cin moriyarta a masana'antar Kannywood.[5] A cikin wata hira da jaruma Farida Jallal ta bayyana cewa a halin yanzu tana mai da hankali kan waƙoƙin Bisharar Musulunci.[6][7][8]

Fina-finai

gyara sashe

Farida Jalal ta zayyano waɗansu finafinai da tayi. Sun haɗa da;

  • Sansani
  • Yakana
  • Raga
  • Jan Kunne
  • Farashi
  • Dan Zaki
  • Lugga
  • Tutarso
  • Namshaza
  • Gidauniya
  • Kumbo.

Da sauransu da dama a cewar ta.[9]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Farida tayi aure ta haifi ƴaƴa biyu, amma ɗaya daga cikin ‘ya’yanta ya rasu. Farida bata da aure a halin yanzu.[ana buƙatar hujja]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Opera News Detail". lucky-wap-ams.op-mobile.opera.com. Retrieved 2022-04-23.
  2. "Har yanzu ba a dena yayinmu ba, Tsohuwar jarumar Kannywood - Farida Jalal". HausalLoaded.Com (in Turanci). 2022-04-22. Retrieved 2022-04-23.
  3. "The 'second coming' of Kannywood". A Tunanina... (in Turanci). 2011-06-26. Retrieved 2022-04-23.
  4. "Farida Jalal Ta Dawo Fim Ne ?". HausalLoaded.Com (in Turanci). 2019-10-03. Retrieved 2022-04-23.
  5. "...Daga Bakin Mai Ita tare da Farida Jalal". BBC News Hausa. 2022-04-21. Retrieved 2022-04-23.
  6. "Har yanzu ba a dena yayinmu ba, Tsohuwar jarumar Kannywood, Farida Jalal". HausaDrop.com (in Turanci). 2022-04-21. Retrieved 2022-04-23.[permanent dead link]
  7. Blueprint (2021-12-24). "I have no regrets going into Islamic songs – FARIDA JALAL". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2022-04-23.
  8. "Why I ventured into Islamic gospel – Farida Jalal". Daily Trust (in Turanci). 2021-09-11. Retrieved 2022-04-23.
  9. https://dailytrust.com/why-i-ventured-into-islamic-gospel-farida-jalal