Ernest Ikoli
Ernest Ikoli Dan siyasa ne a Nigeria, Mai kishin kasa kuma shaharren Dan Jarida. Shine edita na farko a jaridar (Daily Times). Shine kuma shugaban Kungiyan Matasa Ta Nigeria, (Nigerian Youth Movement). A shekarar 1942 ya wakilci jihar legas a majalisa.[1]
Farakon rayuwa da karatu gyara sashe
An Haifi Ikoli a Nembe Wanda take jihar Bayelsa A yanzu.
Yayi karatu a makarantar gomnatin jihar Rivers inda yaka rayin karatun a (King's College Lagos). Bayan gama karatun shi ya zama mai karantarwa a makarantar. Inda daga bisani ya bari ya koma aikin jarida. A yau ana tuna Ikoli a cikin manyan yan jaridun kasan nan da kuma wanda suka bata gudumawa wajen samun yancin Kai.