Eno James Ibanga
Eno James Ibanga saurara, masanin ilimin Najeriya ne. Shi farfesa ne a fannin kimiyyar lissafi/materials science. Yana aiki a matsayin mataimakin shugaban Jami'ar Jihar Akwa Ibom (AKSU). A ranar 3 ga watan Agusta 2020, Mai Girma Gwamna Udom Gabriel Emmanuel ya naɗa Farfesa Eno James Ibanga a matsayin kwamishina a ma'aikatar ayyuka da kashe gobara. Yana da aure da ƴaƴa.
Eno James Ibanga | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Najeriya, Nsukka |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Malami da physicist (en) |
Ilimi
gyara sasheJames Ibanga ya samu digirin digirgir a fannin kimiyyar lissafi ta Solid State a shekarar 2000 a jami'ar Najeriya dake Nsukka.
Sana'a
gyara sasheIbanga ya fara aikinsa a matsayin malamin jami'a a jami'ar Calabar a shekarar 1982. An naɗa shi Farfesa a fannin Physics a Jami’ar Uyo a shekarar 2008 da kuma Shugaban Sashen fannin, Physics da Shugaban Harkokin Ɗalibai. Ibanga malamin Physics ne. Ya kasance Mataimakin Farfesa a Jami'ar Jihar Nassarawa, Keffi, a 2004, kuma Babban Malami, Jami'ar Aikin Noma, Makurdi a 2002. Ya yi koyarwa a Jami’ar Aikin Gona ta Abeokuta a shekarar 1986.
Ibanga ya kasance malami mai ziyara a cibiyoyi daban-daban ciki har da Jami'ar Jihar Akwa Ibom daga 2009 - 2013, Jami'ar Jihar Benue, Makurɗi, 2006-2011 da Jami'ar Agriculture, Makurdi, 2007-2010. Ma'aikacin jarrabawar waje ne a Jami'ar Abuja; Ladoke Akintola University of Science and Technology, Ogbomosho; Jami'ar Ilorin da Jami'ar Obafemi Awolowo. Ya kasance memba a Majalisar Dattawa, Boards da kwamitoci a waɗannan Jami'o'in. Ya yi hidima a NUCa matsayin memba, sannan kuma shugaban kwamitin tantance shirye-shiryen digiri a fannin (Physical Sciences).
Manazarta
gyara sashe- "Akwa Ibom State University". www.aksu.edu.ng (in Turanci). Archived from the original on 11 April 2018. Retrieved 11 April 2018.