Emmanuel Osodeke
Emmanuel Victor Osodeke Farfesa ne na Kimiyyar Ƙasa na Najeriya a Jami'ar Aikin Noma ta Michael Okpara, Umudike,[1] wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa.[2][3] Ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙungiyar a wa'adin da ya gabata.[2]
Emmanuel Osodeke | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Wurin haihuwa | jahar Delta |
Harsuna | Turanci da Pidgin na Najeriya |
Sana'a | researcher (en) da university teacher (en) |
Mai aiki | Jami'ar Jihar Delta, Abraka da Jami'ar Calabar |
Ilimi a | Jami'ar jihar Riba s, Jami'ar Ibadan da Michael Okpara University of Agriculture |
Academic major (en) | soil science (en) |
Hair color (en) | black hair (en) |
Mamba na | Haɗakar Ƙungiyoyin Ma'aikatun Jami'o'i |
Personal pronoun (en) | L485 |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Osodeke a Kokori, ƙaramar hukumar Ethiope ta gabas ta jihar Delta. Ya yi karatun BSc a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ribas a cikin shekarar 1987, sannan kuma ya yi digirin digirgir a Jami’ar Ibadan a cikin shekarar 1989. Ya samu Diploma a fannin Agro-meteorology a Cibiyar Nazarin Yanayin Ƙasa ta Isra’ila a shekarar 1994, sannan a shekarar 2002, ya samu PhD a Jami’ar Aikin Gona ta Michael Okpara da ke Umudike.[4]
Sana'a
gyara sasheOsodeke malami ne a Jami’ar Jihar Delta, Abraka, ya kuma kasance shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i a Jami’ar noma ta Michael Okpara, Umudike. Shi malami ne mai ziyara a Jami'ar Calabar da Jami'ar Cape Cost, Ghana.[4] A ranar 30 ga watan Mayun 2021 an zaɓe shi shugaban ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa.[5][6]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheOsodeke ya auri Onome Osodeke kuma suna da ƴaƴa huɗu.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://thenationonlineng.net/emmanuel-osodeke-in-the-eye-of-the-storm/
- ↑ 2.0 2.1 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-04-01. Retrieved 2023-04-01.
- ↑ https://punchng.com/osodeke-emerges-new-asuu-president/
- ↑ 4.0 4.1 4.2 https://www.bbc.com/pidgin/tori-57306285
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/464669-breaking-asuu-elects-new-president.html?tztc=1
- ↑ https://www.vanguardngr.com/2021/05/breaking-as-biodun-ogunyemi-bows-out-emmanuel-osodeke-emerges-new-asuu-president/