Emamode Edosio
Emamode Edosio,[1] wadda aka fi sani da Ema, ƴar fim ce ta Najeriya kuma darektan fina-finai.[2] Ta samu digirin farko na Kimiyya (B.Sc.) a fannin Computer Science a Jami'ar Jihar Ogun. Ta karanci yin fina-finai na dijital a New York Film Academy (NYFA) da kuma hotunan masu motsi-(motion pictures) a Cibiyar Hotunan Motsi ta Michigan, Amurka. Ta sami kyautar best Film and Director of the year by sisterhood award.[2]
Emamode Edosio | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Emamode Edosio | ||
Haihuwa | Najeriya, 20 century | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Olabisi Onabanjo Digiri a kimiyya Loral Nursery and Primary School, Festac town, Lagos (en) Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Odogbolu New York Film Academy (en) : Digital Film Academy (en) Motion Picture Institute (en) | ||
Matakin karatu | Digiri a kimiyya | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | darakta, filmmaker (en) , music video director (en) da Mai daukar hotor shirin fim | ||
Employers |
Hip Hop TV (en) Ebonylife TV (en) | ||
Muhimman ayyuka | Kasala (en) | ||
Imani | |||
Addini | Kiristanci | ||
IMDb | nm8061992 | ||
emaedosio.com |
A shekarar 2013 ta dawo Najeriya. Ta yi aiki tare da kamfanin samar da fina-finai kamar kamfanin, 66 Dimension is 2007. Daga baya ta yi aiki tare da Hip Hop TV, Clarence Peters a Capital Dreams Pictures, Ebonylife TV kuma a matsayin edita a BBC. Ema ta koma makaranta a Abuja don ƙara karatun a fannin fina-finai. Ta shirya fina-finai da yawa kamar "Joy Ride", "Ochuko" da bada umarnin a shirin fim mai suna, Kasala.
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Edosio a cikin gidan Kirista. Ita ce ta uku a cikin 'ya'yan bakwai da ke gidansu. Mahaifinta masanin gine-gine ne mai ritaya kuma mahaifiyarta lauya ce. Ta fara karatunta ne a makarantar, Loral Nursery and Primary School, Festac town, Legas daga baya ta wuce Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Odogbolu na wasu shekaru kafin ta kammala karatunta na sakandare a S-tee Private Academy, Festac Town.
Ta sami digirin farko (B.Sc.) a fannin kimiyyar na'ura mai kwakwalwa (Computer Science) daga Jami'ar Olabisi Onabanjo, kafin ta tafi karatu a fannin shirya fina-finai na dijital a NYFA da motion pictures a Motion Picture Institute of Michigan.[3]
Sana'a
gyara sasheTa dawo Najeriya a shekarar 2013 bayan karatun ilimi a Amurka.[3] A Najeriya, Ema ta yi aiki da 66 Dimension, Hip Hop TV, Clarence Peters a Capital Dreams Pictures, Ebonylife TV da BBC. A matsayin darekta, Ema ta yi aiki tare da fitattun masu fasaha kamar 2Baba, 9ice, Lord of Ajasa, Terry da Rapmanand da sauran su.[1] Aikinta na farko a Ebonylife TV ana kiran hakan da "Heaven"[3]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "I've Done All Sorts To Learn From Men - Ema Edosio". Nigerian Film.com. Retrieved 20 March 2017.
- ↑ 2.0 2.1 Ade-Unuigbe, Adesola (4 November 2014). "BN Exclusive: An In-depth Look at the Star-Studded 50th Birthday Celebration of Media Mogul, Mo Abudu". Bella Naija. Retrieved 21 March 2017.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 "I gave up friends to focus on my career — Edosio". Punch. 31 July 2016. Retrieved 20 March 2017.