Dunama Dabbalemi, ko Dounama Dibbalém, daga daular Sayfawa, shine mai (sarki) daular Kanem, a cikin Cadi na yanzu, daga 1210 zuwa 1224.

Dunama Dabbalemi
Rayuwa
Mutuwa 1248 (Gregorian)
Yare Daular Sayfawa
Sana'a
Sana'a sarki

Musulmin kwarai ne, Dabbalemi ya fara mu'amala da diflomasiya tare da sarakunan dake Arewacin Afirka kuma daga baya ya shirya wani rukunin masaukin baki na musamman a Alkahira don sauƙaƙe ma Alhazawa aikin hajji zuwa Makka . Har wayau kuma tarihin Ibn Khaldun, ya ambace shi a matsayin "Sarkin Daular Borno", an samu rahoton wani jakaden borno a 1257 zuwa ga Tunisia . [1] A zamanin mulkinsa, ya ayyana jihadi a kan kabilun da ke kewaye da shi kuma ya tsawaita tsawan lokaci da zai bi dan ya mamaye su, bayan hakn ne ya samu dakaru masu karfi mahaya doki su 40,000. Bayan haɓaka yankinsu sun je sun kewaye tafkin Chadi a yankin Fezzan (a cikin Libya na yau) wanda garin ya fada a ƙarƙashin ikon mulkinsa na Kanem, kuma tasirin masarautar ya bazu zuwa yamma da Kano (a cikin Najeriya ta yau), gabas zuwa Ouaddaï, kuma kudu zuwa Adamawa (a yau yankin Kamaru ). Ta hanyar yaƙe-yaƙe, ya kama bayi da yawa waɗanda ya sayar wa yan kasuwan Afirka ta Arewa a matsayin babban abin kasuwancin a cinikin Sahara. [2]

An kuma bashi lambar yabo akan kashe wani dodo dayi, wanda aka ce dodon yana da makurar karfi da tsafi gagara misali, ya kashe dodon yana mai yin izina kan cewa hakan yazama misali akan addinin muslunci na maguzanci, Matakin ya haifar da wasu kalamai na cece kuce, kamar yadda aka ruwaito cewa kashe dodon ya bude wato kofa ta takaddama a tsakanin masarautar. [3]

Dabbalemi ya kirkiro da tsarin baiwa kwamandojin sojojin sa ladan cikakkiyar iko akan mutanen da suka ci nasara akan su. Wannan tsarin, duk da haka, ya jawo matsala domin kwamandojin suna baiwa yaran su gadon garin da suke mulki bayan sun mutu, dabbalemi daga baya hakan ya jawo mai matsala har ya so ya watsar da wannan tsarin amman ina lokaci ya kure. Dabbalemi ya so ya murkushe wannan tunanin, amma sai ya fashe bayan mutuwarsa,hakan ya haifar da asarar yawancin nasarar Dabbalemi.

Diddigin bayanai

gyara sashe
  1. Levtzion/Hopkins, Corpus, 337.
  2. Barkindo, ""Early states", 237-9.
  3. Lange, "Mune-symbol", 84-104.
Janar

Duba ka gani

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe