Desire Oparanozie

'Yar Najeriya wacce take buga wasan kwallon kafa na mata

Ugochi Desire Oparanozie (an haife ta a ranar 17 ga watan Disamba shekarar 1993) Yar'Najeriya ce, wacce take buga wasan kwallon kafa na mata ƙwallon ƙafa amatsayin yar'wasan gaba, tana buga wasa a Division 1 Féminine ma ƙungiyar Guingamp da kuma ƙungiyar wasan kwallon kafa na matan Najeriya.

Desire Oparanozie
Rayuwa
Haihuwa Owerri, 17 Disamba 1993 (30 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa da ɗan wasan kwaikwayo
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Bayelsa Queens (en) Fassara-2010
  Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya2010-
Delta Queens (en) Fassara2010-2012
Lüleburgaz 39 Spor (en) Fassaraga Janairu, 2011-ga Maris, 2011
WFC Rossiyanka (en) Fassara2012-2013112
  VfL Wolfsburg (en) Fassara2013-201410
Ataşehir Belediyesi SK (en) Fassara1 ga Faburairu, 2014-ga Yuli, 201476
  En avant Guingamp (en) Fassaraga Yuli, 2014-5732
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Tsayi 169 cm
Desire Oparanozie

Mataki a duniya

gyara sashe

Oparanozie takasance yar'wasan ƙungiyar Nigerian national team, a inda tare da ƙungiyar ta buga gasar FIFA Women's World Cup na shekarar 2011 da ta shekara 2015.[1][2] Amatsayinta ta matashiya wacce ta fara buga gasar 2010 FIFA U-20 Women's World Cup taci ƙwallaye 2 da kuma ƙwallaye 3 a gasar 2012 FIFA U-20 Women's World Cup.[3][4]

Oparanozie ta kuma sake kasancewa acikin yar'wasan Najeriya a gasar African Women's Championship na 2010 da 2014, da 2016 da kuma na 2018 a inda da ita aka lashe dukkanin gasar hudu sannan kuma taci wani ƙayatacciyar free a wasan karshe na gasar shekarar 2014.[5][6]

Matakin kulub

gyara sashe
 
Desire Oparanozie sanda take buga wasa a Ataşehir Belediyespor a wasansa gida da Kdz. Ereğlispor (2013–14)

Oparanozie ta fara wasan ta ne a kulub ɗin Bayelsa Queens a gasar Nigerian Women's Championship sannan ta koma Delta Queens a 2010. Sannan kuma tayi watanni 2 amatsayin aro ga Kulub ɗin Düvenciler Lisesispor wanda suke buga gasar Turkish Women's First Football League a 2011, sannan daga bisani ta dawo Delta Queens.[7]

A 2012, ta koma Kulub Rossiyanka a Russian Women's Football Championship, tare dasu ta buga wasa hudu na gasar 2012–13 UEFA Women's Champions League, kuma taci ƙwallo daya.[8]

Oparanozie ta koma kulub Bundesliga na VfL Wolfsburg a kakan wasa na 2013–14 a wani kwantaragi da tayi na shekara biyu.[9][10] A rabin kakan na farko, ta buga wasa daya ne kawai, inda ta buga yawancin wasa ma kulub Wolfsburg na biyu. Bayan ƙare rabin kakar ta bar ƙungiyar Wolfsburg.[11] A 21 February 2014, Oparanozie ta koma kulub Ataşehir Belediyespor dan ta cigaba da bugawa wasa a kaka ta biyi na Turkish Women's First Football League.[12]

 
Desire Oparanozie
 
Desire Oparanozie

Sannan a kakan wasa na 2014–15 ta koma Guingamp sake wasa a French Division 1 Féminine,[7] inda ta hadu da wacce take riƙe kambun kungiyar mata ta Najeriya Evelyn Nwabuoku a kaka mai kamawa, wacce takasance yar'uwar Oparanozie ce.[13]

Ƙyautuka

gyara sashe
Najeriya
Tasamu
Delta Queens

Manazarta

gyara sashe
  1. "Canada and Nigeria seek consolation win". FIFA. 4 July 2011. Archived from the original on 8 June 2019. Retrieved 10 November 2016.
  2. "Oparanozie: No words to explain this feeling". FIFA. 9 June 2015. Archived from the original on 11 November 2016. Retrieved 10 November 2016.
  3. "Players – Top goals". FIFA. Archived from the original on 27 March 2019. Retrieved 10 November 2016.
  4. "Players – Top goals". FIFA. Archived from the original on 27 March 2019. Retrieved 10 November 2016.
  5. "African International Competitions". BBC Sport. Retrieved 10 November 2016.
  6. "Nigeria reclaim African women's title". BBC Sport. 25 October 2014. Retrieved 10 November 2016.
  7. 7.0 7.1 "Desire Oparanozie transfers" (in German). SoccerDonna.de. Retrieved 30 June 2015.CS1 maint: unrecognized language (link)
  8. "Player Champions League profile". UEFA. Retrieved 30 June 2015.
  9. "Neue Angreiferin" (in German). vfl-wolfsburg.de. 19 June 2013. Retrieved 13 June 2013.CS1 maint: unrecognized language (link)
  10. Juchem, Markus (13 June 2013). "VfL Wolfsburg verpflichtet Desire Oparanozie". WomenSoccer. Archived from the original on 28 March 2016. Retrieved 10 November 2016.
  11. Juchem, Markus (23 January 2014). "VfL Wolfsburg trennt sich von Desire Oparanozie". WomenSoccer. Archived from the original on 28 March 2016. Retrieved 10 November 2016.
  12. "Futbolcular-Ugochi Desire Oparanozie" (in Turkish). Türkiye Futbol Federasyonu. Retrieved 10 March 2014.CS1 maint: unrecognized language (link)
  13. Shittu, Ibtoye. "INTERVIEW: Nwabuoku speaks on the development of female football". Naij. Retrieved 10 November 2016.