Derek Keir
Derek Keir (an haife shi a shekara ta 1979 Johannesburg, Afirka ta Kudu) ya kasance mataimakin farfesa a fannin ilimin lissafi a Jami'ar Southampton tun daga shekarun 2015. A cikin shekarar 2013 ya sami lambar yabo ta Bullerwell Lecture[1] daga Ƙungiyar Geophysical ta Biritaniya (BGA) don gagarumar gudunmawa ga ilimin lissafi.
Derek Keir | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Johannesburg, 1979 (44/45 shekaru) |
ƙasa | Afirka ta kudu |
Karatu | |
Makaranta | Royal Holloway, University of London (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | scientist (en) da researcher (en) |
Employers | University of Southampton (en) |
Ilimi da aiki
gyara sasheA shekarun 1998-2002 ya karanci ilimin geology da geophysics a Imperial College London, da samun MSc (aji na farko). Ya gudanar da PhD ɗin sa a fannin (Tectonics da Seismology) a lokacin shekarun 2002-2006 a Jami'ar Royal Holloway ta London. Ya kuma gudanar da Teaching Fellowship a Geology a Royal Holloway a wannan lokacin. Kundin karatunsa ya kasance kan ayyukan girgizar kasa na yankin Gabashin Afirka.[2]
A cikin shekarar 2007 ya koma Jami'ar Leeds a matsayin fellow na Binciken Muhalli na Halitta (Natural Environment Research Council) (NERC) kuma a matsayin fellow na Koyarwa a Geology.[3]
An nadya Keir a matsayin malami a fannin Kimiyyar Duniya a Jami'ar Southampton a shekarar 2011 kuma ya zama Mataimakin Farfesa a Geophysics a shekarar 2015.
Babban gudummawar da ya bayar ga kimiyya ita ce nazarin yadda nahiyoyin ke wargajewa ta hanyar nazarin girgizar kasa da ayyukan volcanic na Triangle Afar. Ya yi bincike a kan tsaunuka masu yawa a Habasha da Eritriya, ciki har da Corbetti, Dutsen Ayalu,[4] Adwa (volcano), Erta Ale, Dabbahu Volcano, Dallol, da Nabro Volcano.Wright, TJ; Ebinger, C; Biggs, J; Ayele, A; Yirgu, G; Keir, D; Stork, A (July 2006). "Magma-maintained rift segmentation at continental rupture in the 2005 Afar dyking episode". Nature. 442 (7100): 291–294. Bibcode:2006Natur.442..291W. doi:10.1038/nature04978. hdl:2158/1078052. PMID 16855588. S2CID 4319443. Ya gudanar da yawancin bincikensa tare da haɗin gwiwar Kathryn Whaler da Ian Bastow.[5]
Kyauta
gyara sashe- Kyautar Lecturer ta 2013 Bullerwell-Ƙungiyar Geophysical ta Biritaniya
- 2011 Jason Morgan Kyautar Aikin Farko-Ƙungiyar Geophysical ta Amurka
- 2007 Kyautar Shugaban Ƙasa- Ƙungiyar Geological Society of London
Duba kuma
gyara sashe- Plate tectonics
- Volcanism
Manazarta
gyara sashe- ↑ Bullerwell Lecturers and Lectures". 7 June 2023
- ↑ "Dr Derek Keir | Ocean and Earth Science, National Oceanography Centre Southampton | University of Southampton". www.southampton.ac.uk. Univ. of Southampton. Retrieved 11 April 2019.
- ↑ Keir, D; Pagli, C; Bastow, I; Ayele, A (March 2011). "The magma-assisted removal of Arabia in Afar: Evidence from dike injection in the Ethiopian rift captured using InSAR and seismicity". Tectonics. 30 (2): n/a. Bibcode:2011Tecto..30.2008K. doi:10.1029/2010TC002785. hdl:11568/500499.
- ↑ Keir, D; Pagli, C; Bastow, I; Ayele, A (March 2011). "The magma-assisted removal of Arabia in Afar: Evidence from dike injection in the Ethiopian rift captured using InSAR and seismicity". Tectonics. 30 (2): n/a. Bibcode:2011Tecto..30.2008K. doi:10.1029/2010TC002785. hdl:11568/500499
- ↑ Nobile, A; Pagli, C; Keir, D; Wright, TJ; Ayele, A; Ruch, J; Acocella, A (October 2012). "Dike-fault interaction during the 2004 Dallol intrusion at the northern edge of the Erta Ale Ridge (Afar, Ethiopia)" (PDF). Geophysical Research Letters. 39 (19): n/a. Bibcode:2012GeoRL..3919305N. doi:10.1029/2012GL053152. hdl:11568/500305. S2CID 54908652.