Dele Odule
Dele Odule (an haife shi a 23 ga watan Nuwamba, 1961) ɗan wasan fina-finan Najeriya ne kuma furodusa.[1] An zabe shi a cikin "Best Supporting Actor ( Yoruba )" a 2014 Best of Nollywood Awards saboda rawar da ya taka a fim din Kori Koto.[2] A halin yanzu yana aiki a matsayin shugaban kungiyar masu fasahar fina-finai da wasan kwaikwayo ta Najeriya wato Arts and Movie Practitioners Association of Nigeria.[3]
Dele Odule | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ile Ife, 23 Nuwamba, 1961 (63 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ibadan Bachelor of Arts (en) : theater arts (en) |
Harsuna |
Turanci Yarbanci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, darakta, mai tsara fim da film screenwriter (en) |
Kyaututtuka | |
IMDb | nm2102029 |
Kuruciya da ilimi
gyara sasheAn haifi Odule a garin Oru Ijebu, cikin karamar hukumar Ijebu ta Arewa ta jihar Ogun a shekarar 1961,[4] inda ya yi karatunsa na farko da na sakandare. Ya mallaki takardar shedar Grade II daga Kwalejin Horar da Malamai ta Oru kafin ya wuce Jami'ar Ibadan ta Jihar Oyo[5] inda ya karanta fannin wasan kwaikwayo.[6]
Sana'a
gyara sasheDele ya fara wasan kwaikwayo ne daga wata kungiyar wasan kwaikwayo mai suna Oloko Theater Group karkashin jagorancin Mukaila Adebisi. Ya fito a karon farko a shekarar 1986 kafin a haska bayan ya fito a fim din mai suna Ti Oluwa Ni Ile . Tun daga nan ya ci gaba da taka rawa a fina-finai sama da 200. [6]
zababbun fina-finai
gyara sashe- Ti Oluwa Ni Ile (1993)
- Lakunle Alagbe (1997)
- Oduduwa (2000)
- Afonja (2002)
- Olorire (2003)
- Ògédé Didùn (2003)
- Ogbologbo (2003)
- Suku Suku Bam Bam (2004)
- Omo Olè (2004)
- Iwe Akosile (2005)
- Idajo Mi Tide (2005)
- Eru Ife (2005)
- Ó kojá Ofin (2007)
- Aye Ibironke (2007)
- Bolode O'ku (2009)
- Aworo (2012)
- The Ghost and the Tout (2018)
- Survival of Jelili (2019)
- Kakanfo (2020)
- The New Patriots (2020)
Kyaututtuka da naɗi
gyara sasheShekara | Bikin bayar da kyaututtuka | Kyauta | Sakamako | Ref |
---|---|---|---|---|
2014 | 2014 Best of Nollywood Awards | Best Supporting Actor (Yoruba) | Ayyanawa | |
2014 Yoruba Movie Academy Awards | ||||
2020 | Best of Nollywood Awards | Best Supporting Actor –Yoruba | Ayyanawa |
Duba kuma
gyara sashe- Jerin masu shirya fina-finan Najeriya
- Jerin mutanen Yarbawa
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Dele Odule on IMDb
Manazarta
gyara sashe- ↑ Kayode-Adedeji, Dimeji (21 December 2014). "Dele Odule, Antar Laniyan, Fathia Balogun others head breakaway Yoruba movie association". Premium Times. Retrieved 4 December 2015.
- ↑ "Best Of Nollywood Awards releases nominees' list". Ecomium Magazine. 14 August 2014. Retrieved 4 December 2015.
- ↑ Showemimo, Dayo (22 December 2014). "Dele Odule emerges new president of TAMPAN". Nigeria Entertainment Today. Retrieved 4 December 2015.
- ↑ "Dele Odule". Nigerian celebrities. January 9, 2016. Archived from the original on October 13, 2020. Retrieved December 24, 2021.
- ↑ "ALL NOLLYWOOD ACTORS & ACTRESSES & BRIEF INTRODUCTION & BIOGRAPHY". Daily Mail (Nigeria). 3 September 2014. Archived from the original on 5 November 2016. Retrieved 4 December 2015.
- ↑ 6.0 6.1 "Dele Odule". Retrieved 4 December 2015.