Davidson Andeh

Dan Wasan kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya

Davidson Andeh (an haife shi ranar 17 ga watan Janairun, 1958). dan dambe mai ritaya ne, daga Najeriya, wanda ya lashe kambun duniya a rukunin marasa nauyi na (– 60 kg) a Gasar Cin Kofin Duniya na Biyu, wanda aka gudanar a Belgrade, Yugoslavia. A karshe yaci Vladimir Sorokin daga Tarayyar Soviet.[ana buƙatar hujja]

Davidson Andeh
Rayuwa
Haihuwa Lagos, 17 ga Janairu, 1958 (66 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Ahali Anthony Andeh
Sana'a
Sana'a boxer (en) Fassara
Tsayi 180 cm

Wakilci gyara sashe

Andeh ya wakilci kasarsa ta haihuwa a Gasar Olympics ta bazara ta shekaran 1976 a Montreal, Quebec, Kanada, amma Najeriya tayi fice daga gasar saboda halartar New Zealand, don haka nasara a zagayen farko na rukunin featherweight ( – 57 kg) an bai wa Rai Sik na Indiya . [1]

Kwararre gyara sashe

Andeh ya zama ƙwararre a cikin shekaran 1980, kuma ya karɓi taken Afirka mai nauyi a cikin shekaran 1983 ta hanyar doke Tapsoga Tiga na Togo . Ya yi ritaya daga gasar a shekaran 1987, tare da rikodin din nasarori 18 (buga ƙwanƙwasa 12), hasara biyar da fafatawa ɗaya.

Hanyoyin waje gyara sashe

  • Boxing record for Davidson Andeh from BoxRec

Manazarta gyara sashe

  1. Official 1976 Olympic Report p153, Vol 3