Dauda Kako Are
Dauda Kako Are (an haifeshi ranar 11 ga watan Yuli, 1959)[1] akawu ne kuma ɗan siyasa. Dan Majalisar Wakilan Najeriya ne mai wakiltar mazaɓar Mushin I bayan ya zama zakara a zaɓen Najeriya na 2015 a watan Afrilu a ƙarƙashin jam'iyyar Accord Party.[2][3]
Dauda Kako Are | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011 | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Lagos,, 11 ga Yuli, 1959 (65 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta | Jami'ar jahar Lagos Digiri a kimiyya : accounting (en) | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa da accountant (en) | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa | Action Alliance (en) |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Kako Are, ranar 11 ga watan Yuli, na shekara ta alif ɗari tara da hamsin da tara 1959, a birnin Lagos na Najeriya. Ya halarci Makarantar Sakandare ta Baptist, Saki, Jihar Oyo inda ya samu shaidar kammala karatunsa na Senior School a shekara ta alif ɗari tara da saba'in da bakwai 1977. Ya wuce Jami'ar Legas, Akoka inda ya yi digirinsa na farko a fannin (Accounting) a shekarar alif ɗari tara da tamanin da biyar 1985.
Fagen Siyasa
gyara sasheKako Are dai ya fara harkar siyasa ne a shekarar alif ɗari tara da casa'in da tara 1999 bayan an zaɓe shi a matsayin wakilin mazaɓarsa a majalisar dokokin jihar Legas daga 1999 zuwa 2003 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Action Congress of Nigeria. Ya tsaya takarar majalisar wakilai ta tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar Accord Party (A) kuma ya lashe zaɓen a matsayin mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Mushin I a babban zaben Najeriya na 2015.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Nigeria, Media (2018-06-05). "Biography Of Dauda Kako Are". Media Nigeria (in Turanci). Retrieved 2020-07-08.
- ↑ Admin (2016-11-15). "ARE,Hon. Abayomi Dauda Kako". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). Retrieved 2020-07-08.
- ↑ "Rep attributes victory to confidence, trust of electorate". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2015-04-14. Retrieved 2020-07-08.