Ɗan'ice
Ɗan'ice da yawa ƴa'ƴan itace ko ƴa'ƴan itatuwa, a Ilimin botany, Ɗan'ice wani nau'in ɓangaren shuka ne, dake dauke da iri na flowering plant (wanda aka fi sani da angiosperms) kuma yana girma ne daga cikin ovary bayan yin tohonsa flowering.
dan-ice | |
---|---|
botanical term (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | plant organ (en) da plant ovary (en) |
Bangare na | Angiosperms (en) |
Facet of (en) | plant anatomy (en) |
Develops from (en) | gynoecium (en) |
Has characteristic (en) | type of fruit (en) |
Daga ya'yan itace ne ake samun iri na shuka dan a sake nomawa. Ya'yan itatuwan da ake ci, musamman a wasu lokutan sun sanya cigaba da rayuwa yan'adam data dabbobi ta hanyar taimakekeniya wato symbiotic relationship da hanyar samun yawaitar iri da nutrition; a takaice, mutane da dabbobi sun dogara ne kacokan akan ya'yan itace a matsayin hanyar samun abinci.[1] hakan yasa, ya'yan itace suka dauki babban kaso a yawan amfanin goma da ake samu a duniya, kamar su ( apple da pomegranate).
A ilimance idan ance, "dan-ice" to ana nufin tsiron da itaciya ke fitarwa daga jikin ta ne wanda keda zaki ko tsami, kuma za'a iya sha ko amfani dashi a yadda yake batare da an dafa ko masa wani abu ba, sune kamar apple, ayaba, inibi, lemun tsami, lemun zaƙi, da strawberries. A wani bangaren amfani da kalmar, "dan-ice" yahada da abubuwa da dama wadanda ma ba'a kiransu da "ya'yan ice", kamar su wake, masara kernels, timatir, da hatsin alkama.[2][3] haka kuma sashen fungus da ke samar da spore da suna wurin jikin.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Lewis, Robert A. (2002). CRC Dictionary of Agricultural Sciences. CRC Press. ISBN 978-0-8493-2327-0.
- ↑ Schlegel, Rolf H J (2003). Encyclopedic Dictionary of Plant Breeding and Related Subjects. Haworth Press. p. 177. ISBN 978-1-56022-950-6.
- ↑ Mauseth, James D. (2003). Botany: An Introduction to Plant Biology. Jones and Bartlett. pp. 271–72. ISBN 978-0-7637-2134-3.
- ↑ "Sporophore from Encyclopædia Britannica". Archived from the original on 2011-02-22. Unknown parameter
|deadurl=
ignored (|url-status=
suggested) (help)