Christy Obekpa
Christy Obekpa yanzu Mrs Aremu (an haife tana ranar sha biyar 15 ga watan Disamba, shekarar alif dari tara da saba'in da daya miladiyya 1971), ta kasan ce yar wasan judoka ce ta Najeriya wacce ta shiga gasar ajin mata masu matsakaicin nauyi. Ta lashe lambar tagulla a wasannin Commonwealth Judo na 1990 da lambar azurfa a Gasar Judo ta 1992 CW . Misis Aremu ita ce mace ta farko da ta lashe lambar yabo ta judo Commonwealth. Ta kuma lashe lambobin tagulla biyu a Wasannin Afirka na 1999 da lambar tagulla a Gasar Judo ta Afirka ta 2000.
Christy Obekpa | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Najeriya, 15 Disamba 1971 (53 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Harshen, Ibo |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | judoka (en) |
Aikin wasanni
gyara sasheA cikin 1990, a Gasar Commonwealth Judo da aka gudanar a Auckland, New Zealand . Ta halarci gasar kilo 72 inda ta lashe lambar tagulla. A Gasar Commonwealth Judo ta 1992 da aka gudanar a Cardiff, Wales . Ta kuma halarci kuma ta lashe lambar azurfa a bikin kilo 72.