Chioma Ikokwu (an haife ta a ranar 25 ga watan Yunin,shekara ta 1989A.c) wacce aka fi sani da Chioma Goodhair lauya ce ta kasar Najeriya, ’yar kasuwa kuma kocin zartarwa. Ita ce mai haɗin gwiwa kuma Shugaba ta Good Hair Ltd da Brass and Copper Restaurant & Lounge, [1] [2] tare da Kika Osunde. [3] Ita ce ta kafa gidauniyar The Good Way Foundation, kungiyar da ke mai da hankali kan wayar da kan cutar sikila a matsayin ɗaya daga cikin manyan wuraren da ta fi mayar da hankali.

Chioma Goodhair
Rayuwa
Haihuwa Lagos,, 25 ga Yuni, 1989 (35 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Harshen, Ibo
Karatu
Makaranta University of Birmingham (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a Lauya da reality television participant (en) Fassara
hoton chioma good hair

Ƙuruciya da ilimi.

gyara sashe

An haifi Ikokwu a ranar 25 ga watan Yunin, shekarar 1989 a Legas, Najeriya. Ta halarci Jami'ar Birmingham kuma ta kammala karatu a shekarar 2010, tare da LL. B digiri.[4] Ta gama karatu tare da LL. M digiri a International Environmental Law da International Commercial Arbitration a Jami'ar London (School of Oriental and African Studies) inda ta kammala da bambanci. Ta halarci Makarantar Shari'a ta Najeriya kuma an kira ta zuwa cikin Lauyoyin Najeriya a shekarar 2013.[5]

Bayan ta kammala digiri na biyu a fannin shari'a, ta yi aiki a wani kamfanin shari'a da sasantawa a ƙasar Lebanon a takaice kafin ta koma kasar Najeriya ta halarci makarantar koyon aikin lauya. Ta haɗu da abokin aikinta Kika Osunde [6] a Jami'ar Birmingham[7] inda ta yi aiki a matsayin Sakatariyar zamantakewa ta Jami'ar Birmingham ACS (Afro Caribbean Society). Ta kafa kamfani mai suna Good Hair Ltd wanda aka fara a Ingila a shekarar 2009, kafin ta koma Najeriya a shekarar 2014. [8] Ikokwu da Osunde sun gina wata cibiyar kyan gani da ake kira "The Good Hair Space". [9] Ita ce mai mallakar Brass and Copper, gidan abinci da mashaya a cikin Good Hair Space a Lekki, a garin Legas.[10]

Ita ce wacce ta kafa Chioma Ikokwu Start-up Fund Initiative, wacce ke mai da hankali kan samar da jari ga kananan ‘yan kasuwa tare da sabbin dabaru. Tana gudanar da shirin horarwa na zartarwa inda take ba wa 'yan kasuwa shawara kan ƙirƙirar kasuwanci, yin alama da tallata.[11][12]

Tallafawa.

gyara sashe

Gidauniyarta ta mayar da hankali ne kan kawar da talauci, inganta kiwon lafiya, ilimi da yanayin rayuwa ga marasa galihu a Afirka. Gidauniyar ta yi bincike tare da yaki don rage wa mutanen da cutar sikila ta shafa.[13] Har ila yau, Ikokwu ta kasance wani ɓangare na taron teburi na hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ta mayar da hankali kan wayar da kan jama'a da kula da cutar sikila, kuma gidauniyar Sickle cell ta yankin Afrika da ke garin New York ta ba ta lambar yabo ta jin kai.[14]

Manazarta.

gyara sashe
  1. Guardian Woman (9 May 2020). "'Women have it a lot harder raising capital due to stereotypes, expectations'". Guardian. Archived from the original on 29 September 2020. Retrieved 26 August 2020.Guardian Woman (9 May 2020). " 'Women have it a lot harder raising capital due to stereotypes, expectations' " . Guardian . Retrieved 26 August 2020.
  2. Anonymous (7 February 2018). "Casa Lydia and Cocoon Birth Brass & Copper by the Good Hair Dolls" . Foodie In Lagos. Retrieved 26 August 2020.
  3. Agbo, Njideka (31 May 2020). "Kika Osunde: Luxury, Finesse And Brand Reputation" . Guardian . Retrieved 26 August 2020.
  4. Agbonkhese, Josephine (10 May 2020). "Chioma Ikokwu: My family helped to start my company at age 18" . Vanguard . Retrieved 26 August 2020.
  5. "Chioma GoodHair, Now Chioma Landlady" . This Day Live . 7 April 2019. Retrieved 26 August 2020.
  6. Dokubo, Titi (5 April 2018). "Savage! CHIOMA And KIKA 'Good Hair' Are Hijacking The Lagos Fashion Scene" . Style Rave . Archived from the original on 2020-08-15. Retrieved 5 April 2018.
  7. "How To Launch Your Own Hair Business with Chioma Ikokwu" . sheleadsafrica.org . Archived from the original on 2018-09-21. Retrieved 2020-08-27.
  8. Okeke, Ifeoma (4 December 2017). "How Chioma and Kika grew Good Hair Limited into global brand" . Business Day. Retrieved 26 August 2020.
  9. Rave, Style (11 September 2020). "Let's Talk Style: 31 Questions With Chioma GoodHair" . Style Rave . Retrieved 11 September 2020.
  10. Rave, Style (11 September 2020). "Let's Talk Style: 31 Questions With Chioma GoodHair" . Style Rave . Retrieved 11 September 2020.
  11. Ogunlami, Adetoun (25 June 2020). "7 Things To Know About Chioma 'GoodHair' Ikokwu As She Turns A Year Older" . Fab Woman . Retrieved 26 August 2020.
  12. Bella Naija (12 May 2018). "The Good Hair Merchants! Kika and Chioma cover TW Magazine's Latest Issue" . Bella Naija . Retrieved 26 August 2020.
  13. Viano (28 March 2019). "Kika and Chioma " The Good Hair Girls" Making Waves With Their Sickle Cell Foundation" . Styles with Elovia . Retrieved 26 August 2020.
  14. Viano (28 March 2019). "Kika and Chioma " The Good Hair Girls" Making Waves With Their Sickle Cell Foundation" . Styles with Elovia . Retrieved 26 August 2020.