Charles III
Charles, Yariman Wales (Charles Philip Arthur George; an haife shi a 14 ga watan Nuwanban 1948) shine Magajin Sarautar Biritaniya amatsayin sa na babban yaron Elizabeth II. Yakasance shine Duke na Cornwall da Duke na Rothesay tun daga 1952, kuma shine mafi shekaru kuma wanda yafi dadewa amatsayin sa na magaji mai jiran gado, a tarihin Biritaniya.[1] kuma shine mafi dadewa wanda ya rike Yariman Wales, ya rike tun daga 1958.[2] An haifi Charles a Buckingham Palace amatsayin tattaba kunnen Sarki George VI da uwargidansa Sarauniya Elizabeth. Yayi karatu a makarantun Cheam da Gordonstoun, inda mahaifinsa, Yarima Philip, Duke na Edinburgh, yayi da yake karami, da kuma Timbertop na Makarantar Grammar Geelong dake Victoriya, Australiya. Bayan yasamu digiri na Bachelor of Arts daga Jami'ar Cambridge, Charles yayi aiki a Royal Air Force da Royal Navy daga shekara ta 1971 zuwa 1976. A shekarar 1981, ya auri Budurwa Diana Spencer kuma suna da ya'ya biyu tare: Yarima William (b. 1982)—wanda yazama Duke na Cambridge—da kuma dan'uwansa Yarima Harry (b. 1984)—wanda yazama Duke na Sussex. A 1996, ma'auratan sun rabu, bayan samun junansu da yaudarar juna, ta hulda a wajen aure. Diana ta mutu a hatsarin mota a birnin Paris, shekarar data biyo. A 2005, Charles ya auri budurwarsa da suka dade tare Camilla Parker Bowles.
ManazartaGyara
- ↑ Cite news|title=Prince Charles becomes longest-serving heir apparent|url=https://www.bbc.com/news/uk-13133587%7Cpublisher=BBC News |accessdate=30 Novemb[permanent dead link]er 2011|date=20 April 2011
- ↑ Cite web|last1=Bryan|first1=Nicola|title=Prince Charles is longest-serving Prince of Wales|url=https://www.bbc.com/news/uk-wales-41179772 |publisher=BBC News |accessdate=9 September 2017