Binta Bello, ta kasan ce tsohuwar malama ce, kwamishina a jiha, kuma a yanzu mataimakiyar Marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya. Bello tana wakiltar Mazabar Tarayyar Kaltungo / Shongom ta jihar Gombe. Ita kaɗai ce mace dake shugabancin majalisar Najeriya.[1]

Binta Bello
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019 - Simon Elisha Karu
District: Kaltungo/Shongom
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

6 ga Yuni, 2011 - 6 ga Yuni, 2015
District: Kaltungo/Shongom
Rayuwa
Haihuwa Igbuzo (en) Fassara, 1970 (53/54 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar, Jos
Jami'ar Maiduguri
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Bello a garin Igbuzo, jihar Delta ga mahaifin wani hafsan soja ne.[2] Ta zagaya ko'ina cikin ƙasar kafin daga bisani ta dawo zuwa jiharta ta asali Gombe.[2][3]

Ta samu takardar shaidar karatu na II daga WTC Bajoga, jihar Gombe a shekara ta dubu daya da Dari Tara da tamanin da takwas 1988, difloma a fannin mulki a jami’ar Jos a shekara ta dubu daya da Dari Tara da casa'in da biyar 1995,[3] da kuma B.Sc. a cikin Gudanar da Jama'a daga Jami'ar Maiduguri a shekara ta dubu biyu da goma 2010.[1]

Bello ta yi aiki a matsayin kwamishina mai kula da harkokin mata a jihar Gombe daga shekara ta 2007 zuwa 2010.[4] Daga nan sai ta tsaya takarar Wakiltar Mazabar Tarayya ta Kaltungo / Shongom a karkashin jam'iyyar PDP wacce ta yi nasara.[4] Sauran matan P.D.P da aka zaba sun hada da Nnenna Elendu-Ukeje, Sodaguno Festus Omoni, Nkiruka Chidubem Onyejeocha, Rita Orji, Evelyn Omavovoan Oboro, Beni Butmaklar Langtang, Omosede Igbinedion Gabriella, Stella Obiageli Ngwu da Eucharia Okwunna.[5]

A shekara ta 2019 ta fadi zabe a hannun APC. Amos Bulus jam’iyyar APC mai 80,549 sai PDP mai 63,312.[6]

Manazartai

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "Hon. Binta Bello". Archived from the original on April 22, 2018. Retrieved April 21, 2018.
  2. 2.0 2.1 "Binta Bello: The Amazon in the House". Punch newspaper. Archived from the original on April 22, 2018. Retrieved April 22, 2018.
  3. 3.0 3.1 Goodwill, best recipe for success in politics – Hon Bello, Chair, Women in Parliament". Vanguard News. Archived from the original on April 22, 2018. Retrieved April 22, 2018.
  4. 4.0 4.1 "Binta Bello: The Amazon in the House". Punch newspaper. Archived from the original on April 22, 2018. Retrieved April 22, 2018.
  5. "Jimoh, Abbas (2015-06-06). "Women of the 8th National Assembly". Daily Trust. Retrieved 2020-05-06.
  6. Binta, bello. "Lawmaker empowers 640 women with new skills". THE GUARDIAN. Retrieved 17 December 2017.