Bikin Kalibi biki ne na shekara-shekara da sarakuna da mutanen Sankana, wani gari a gundumar Nadowli-Kaleo da ke Yankin Upper West na Ghana.[1][2] Yawancin lokaci ana yin bikin ne a cikin watan Afrilu.[3][4][5]

Infotaula d'esdevenimentBikin Kalibi
Iri biki
Wuri Nadowli-Kaleo District, Yankin Upper West
Ƙasa Ghana
Nahiya Afirka

Bukukuwa gyara sashe

Yayin bikin, ana maraba da baƙi don raba abinci da abin sha. Mutanen sun sanya tufafin gargajiya kuma akwai durbar sarakuna. Akwai kuma raye -raye da kade -kade.[6]

Muhimmanci gyara sashe

Ana yin wannan biki don tunawa da nasarar da mutanen yankin suka samu akan maharan bayi da Babatu da Samori ke jagoranta a shekara ta 1896.[7] Haka nan kuma ya zama lokacin da ake roƙon kakanni lafiya da wadata.[8]

Manazarta gyara sashe

  1. "UW Deputy Minister emphasises flagship programmes will alleviate poverty". BusinessGhana. Retrieved 2020-08-23.
  2. "Festival Calender [sic]". www.travel-to-discover-ghana.com (in Turanci). Retrieved 2020-08-23.
  3. "Festivals Ghana - Easy Track Ghana". www.easytrackghana.com. Retrieved 2020-08-23.
  4. "Festivals – Slutchtours" (in Turanci). Archived from the original on 2021-01-18. Retrieved 2020-08-23.
  5. "Ghana Festivals". www.ghana.photographers-resource.com. Retrieved 2020-08-23.
  6. "Major Festivals". www.ghanaembassyiran.com. Retrieved 2020-08-21.
  7. "Government to spend on tourist attractions". www.ghanaweb.com. 2001-04-09. Retrieved 2020-08-23.
  8. "National Commission on Culture - Ghana - Upper West Region". www.s158663955.websitehome.co.uk. Retrieved 2020-08-23.