Bikin ART X Legas
ART X Lagos, bikin baje kolin fasaha ne a Lagos, Nigeria. Ita ce bikin baje koli na kasa da kasa na farko a yammacin Afirka,[1][2][3][4] da aka kirkiro kuma, aka kaddamar a cikin 2016,[5][6] kuma an gudanar da karo na shida na ya zuwa yanzu.[7][8] Za a gudanar da bikin baje kolin karo na bakwai daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Nuwamba 2022 a Legas.
Bikin ART X Legas |
---|
ART X Lagos | Salon | Sana'o'in zamani daga Afirka da 'yan kasashen waje | |
---|---|---|---|
Yawanci | Shekara-shekara | ||
Wuri(s) | Lagos, Nigeria | ||
An kaddamar da shi | 2016 | ||
Wanda ya kafa | Tokini Peterside |
Kafuwa da tsari
gyara sasheTokini Peterside ne ya kirkiri ART X Legas a cikin 2016 ta, ɗan kasuwa ne dan Najeriya, don nunawa da tallafawa fasahun zamani na Afirka da ƙasashen waje.[9][6][10] Bikin na ja yawo majiɓintan gida da ɗimbin masu tara kuɗi na ƙasa da ƙasa, masu kula, da masu suka kowace shekara.
ART X Legas al'amari ne na kwanaki hudu, wanda ke nuna wuraren zane-zane a Afirka da kuma baje kolin 'yan kasashen waje da aka kafa da kuma masu fasaha masu tasowa. Baje kolin ya kuma hada da shirin tattaunawa, Tattaunawar ART X, da ke nuna masu magana a cikin gida da na kasashen waje, da kuma ayyukan mu'amala don jan hankalin masu sauraronsa daban-daban, zane-zane da wasan kwaikwayo na kida.[11][12][13][14]
A shekara ta 2020, an gudanar da bikin ART X Legas ta yanar gizo.[15]
ART X Legas ta dawo da bikin baje koli a shekarar 2021, baje kolin na zahiri na farko a Afirka tun bayan barkewar cutar Covid 19.[16]
The seventh edition will be held from 3 to 6 November 2022 in Lagos, Nigeria, with an extension online.
Karo na farko
gyara sasheAn gudanar da bikin ART X Legas a karo na farko daga 4 zuwa 6 ga Nuwamba 2016. Ya nuna fasahar zamani ta fiye da 60 da aka kafa da masu fasaha daga kasashe 10 na Afirka, ciki har da Najeriya, Afirka ta Kudu, Ghana da Mali,[17] kuma Bisi Silva ne ya ba da umarni da fasaha. Baje kolin na farko ya tarbi maziyarta 5,000 daga sassan Najeriya da ma duniya baki daya.[18]
Fitattun mawakan da suka yi wasa a karo na farko sun hada da William Kentridge, Barthelemy Togou, Sokari Douglas-Camp, Ghana Amer, Victor Ehikhamenor, Gerald Chukwuma, Amadou Sanogo, Owusu Ankomah, Jeremiah Quarshie, da Obiageli Okigbo da sauransu.[13] Masu magana a ART X Talks sun hada da El Anatsui, Bruce Onobrakpeya, Prince Yemisi Shyllon, da Zoé Whitley .
Karo na biyu
gyara sasheAn gudanar da karo na biyu daga ranar 3 zuwa 5 ga Nuwamba 2017 kuma an yi maraba da maziyarta fiye da 9,000 don ganin ayyukan masu fasaha daga kasashe sama da 15 na Afirka.[12]
Bikin baje kolin ya hada da manyan hotuna daga Najeriya da Afirka ta Kudu da Ghana da Senegal da Kamaru da Ivory Coast da Mali da kuma Birtaniya. Fitattun mawakan sun hada da Yinka Shonibare (MBE), Zanele Muholi, Modupeola Fadugba, Nandipha Mntambo, Virginia Chihota, Boris Nzebo, Babatunde Olatunji, Pamela Phatsimo Sunstrum, Portia Zvavahera da Lakin Ogunbanwo da sauransu.[18]
Baje kolin ya kuma hada da nune-nunen ayyuka na musamman na masu fasahar solo, wanda Missla Libsekal ta shirya, wanda ya yi fice a ciki akwai baje kolin zane-zanen katako guda bakwai da babban dan zamani na Najeriya Ben Enwonwu ya yi, don tunawa da cikarsa shekaru dari. Masu magana a ART X Talks sun hada da Njideka Akunyili Crosby, Lemi Ghariokwu, Peju Alatise, Stacy Hardy da Wura-Natasha Ogunji.
Karo na uku
gyara sasheAn gudanar da bikin a karo na uku daga ranar 2 zuwa 4 ga Nuwamba 2018, inda aka sake yin maraba da baƙi daga ko'ina cikin duniya, tare da baje kolin ayyuka daga ƙasashe 18. A karon farko, baje kolin ya kunshi nuna masu fasaha da masu baje koli na gabashin Afirka, daga kasashe irin su Kenya, Uganda, da Habasha.
Wani muhimmin abin burgewa a bikin baje kolin na 2018 shi ne baje koli na musamman da Yinka Shonibare CBE ya yi, inda ya binciko muhimman ayyukansa, wanda Missla Libeskal ta shirya. Fitaccen zane na Ben Enwonwu "Tutu" (1974),[19] zane da aka fi siya a wurin gwanjo na Afirka, an kuma nuna shi a wurin taron, ta kasance baje kolinsa na farko a Legas bayan sama da shekaru 40.
Sauran fitattun mawakan sun hada da Cyrus Kabiru, Sokari Douglas Camp CBE, Zanele Muholi, Paul Onditi, Victor Butler, Nike Davies-Okundaye, Tadesse Mesfin, Aboudia, da dai sauransu.
Wadanda suka yi jawabi a muhawara na ART X Talks, sun hada da Yinka Shonibare CBE, Chika Okeke-Agulu, Aboubakar Fofana, Peju Layiwola, HRM Igwe Nnaemeka Alfred Achebe, gami da Meskerem Assegued.
Karo na hudu
gyara sasheAn gudanar da bikin a karo na huɗu daga ranar 1 zuwa 3 ga watan Nuwamba 2019, kuma an karbi baƙi daga ko'ina cikin duniya, tare da zanuka sama da 90 daga ƙasashe 25.[20] Bikin na 2019 ya gabatar da ART X Modern, wani sashe na baje kolin da aka sadaukar don majagaba na fasahar zamani na Afirka daga tsakiyar karni na 20, da kuma Wasanni, wanda ya hada da wasanni uku a karshen makon.
Wani muhimmin al'amari na bajekolin na 2019 shine muhawarar ART X Talks, wanda ya ƙunshi babban jawabi daga Wangechi Mutu. Sauran fitattun masu magana sun hada da Emeka Ogboh, N'Goné Fall, Kathryn Weir, Joel Benson da Reni Folawiyo .
Yusuf Grillo, Ablade Glover, Joy Labinjo, Sam Nhlengethwa, Nelson Makamo, Titza Berhanu, Jems Koko Bi, Demas Nwoko, Lady Skollie, da Uche Okeke na daga cikin fitattun mawakan da aka gabatar a wannan bikin.
Bikin baje kolin ya kunshi ayyuka da dama da suka hada da ayyukan Emeka Ogboh, wanda Tayo Ogunbiyi ya shirya, da kuma wasanni uku da Wura-Natasha Ogungi ya shirya.
Karo na biyar
gyara sasheAn gudanar da bikin a karo na biyar daga 2 zuwa 9 ga watan Disamba 2020, bikin ya karbi baƙunci mutane daga ƙasashe 101 don nuna ayyukansu na zane-zane sama da 200. An gabatar da baje kolin ne akan yanar gizo bisa ARTXLAGOS da aka sake buɗewa. COM kuma an ƙarfafa shirin da kayataccen shirin kallo na kai tsaye a sassa 13 na shirin.
karo na 2020 ya gabatar da New Nigeria Studios,[21] nunin kan yanar gizo wanda ya baje kolin ayyukan wasu zaɓaɓɓun masu daukar hoto, masu shirya fina-finai da masu zanga-zangar da suka fito kan titunan Najeriya a watan Oktoba 2020, da kuma ART X Review - Shirin Wrap Up with Njideka Akunyili Crosby, babban darasi ga masu zane masu tasowa sun tattaunawa game da bunkasawa, wuri da abubuwan da mai zane ke iya yi a duniyar yau.
Wani muhimmin lokaci na bikin 2020 shine muhawara ART X Talks, wanda ya nuna fitaccen mai fasaha Hank Willis Thomas da Opal Tometi, wanda ya kirkiri Black Lives Matter. Sauran fitattun masu magana sun haɗa da Folarin "Falz" Falana, Lola Ogunnaike, Freda Isingoma, Lemi Ghariokwu, Yagazie Emezi and Kelechi Amadi-Obi.[22]
Masu zane da suka halarci taron sun hada da Ouattara Watts, Ben Osawe, François-Xavier Gbré, Ablade Glover, Nike Okundaye Davies, Boris Nzebo, Aboudia, Abe Odedina, Angele Etoundi Essamba, Olu Ajayi, Wole Lagunju da Tiffanie Delune da sauransu.
Shirin baje kolin ya kuma kunshi ART X Live! Inda ya gabatar da "Like Someone's Watching", aikin na musamman akan ra'ayoyin, da kuma "minti 40 tare da...".
Karo na shida
gyara sasheAn gudanar da bikin a karo na shida daga 4 zuwa 7 ga watan Nuwamba 2021 a Fadar Tarayya ta Legas, kuma an tsawaita shirin ta kafar yanar gizo har zuwa 21 ga Nuwamba a ARTXLAGOS. COM Ta yi maraba da manyan gidajen tarihi guda 30, tare da gabatar da zane-zane daga masu fasaha 120 daga Afirka da na kasashen waje.
Shirin ya gabatar da nau'ikan ayyukan da aka tsara, waɗanda suka haɗa da "Future Africa" da "Unfolding Layers of Time" wanda Aude Christel Mgba ya tsara, da kuma wani aikin hulɗar "Muna nan" wanda AWCA ta tsara.[16]
Tattaunawar ART X Talks ya fito da manyan mashahuran masu jawabai ciki har da tattaunawa tare da haɗin gwiwar gidan tarihi na Smithsonian National Museum of African Art. Manyan masu jawabi sun haɗa da Prince Yemisi Shyllon, Kavita Chellaram, Osinachi, Hakeem Adedeji, Bonaventure Soh Bejeng Ndikung, Kelani Abass, Emmanuel Iduma gami da Nengi Omuku .
Mahimman bayanai na baje kolin 2021 sun haɗa da "Reloading...", wani nunin NFT wanda ke nuna 10 daga cikin mafi kyawun zanukan zamani na dijital a Afirka tare da haɗin gwiwar SuperRare, wanda babban mashahurin mai zane-zane na Afirka Osinachi ya tsara, tare da Maurice Chapot da Ayo Lawson[23] da "Art of Yusuf Grillo", gabatarwa ta musamman ta kó don murnar rayuwa da gadon fitaccen ɗan wasan Najeriya Yusuf Grillo.[24]
Masu zane a bikin sun hada da Amoako Boafo, Aboudia, JD 'Okhai Ojeikere, Mous Lamrabat, Benji Reid, Ouattara Watts, Nike Okundaye Davies, Joana Choumali, Boris Nzebo, Anjel (Boris Anje), Dmitri Fagbouhoun da sauransu.
Kyautar Bankin Access a Bikin ART X
gyara sasheKamfanin ART X Lagos ne ya kaddamar da lambar yabo ta ART X, tare da hadin gwiwar bankin Access, domin ba da gudummawa ga ci gaban bunkasar fannin fasahar nune-nune a Najeriya.
Karo na 2016 da 2017 na kyautar sun ta'allaka ne kan matasa masu fasaha, kuma Patrick Akpojotor da Habeeb Andu ne suka lashe gasar.[25][26]
A shekara ta 2018, lambar yabo ta samo asali ne don ƙarfafa ƙoƙarin masu zane masu taso waɗanda suka nuna himma ga ayyuka a matsayin ƙwararrun masu fasahar gani. Bolatito Aderemi-Ibitola, mai fasaha da dama, ya zama zakara a matsayin wanda ya lashe kyautar, inda ya karbi kyautar kudi don aiwatar da wani shiri mai ban sha'awa da kuma gabatar da shi kadai a bugu na ART X Legas na 2018, da kuma zama na watanni uku a Gas Works. a London a 2019.
A cikin shekara ta 2019, an canza sunan lambar yabo zuwa Gasar Bankin Access na Art X wato Access Bank ART X Prize. Mai daukar hoto na labarai wato Etinosa Yvonne ne ya ci nasarar lashe gasar.[27]
Bayan tsagaitawa na dan lokaci a dalilin Covid-19, lambar yabo na bankin Access ART X ta dawo a shekara na 2021, tare da mai zane na zamani Chigozie Obi ta yi nasarar lashe gasar.[28]
Shirin ART X na Kai-Tsaye!
gyara sasheART X na Kai-Tsaye! wani dandali ne na bayyanawa da gwadawa daga ƙwararrun matasa masu ƙirƙira na Afirka, wanda ya kunshu kaɗe-kade da fasaha na zamani, wanda ART X Collective ya ƙaddamar a shekara ta 2016 - waɗanda suka kirkiri ART X Lagos, babban bikin baje kolin fasaha na duniya na yammacin Afirka.
ART X na Kai-Tsaye! wani baje koli ne mai nishadantarwa, wanda ke gudana a yayin bikin baje kolin fasaha na ART X Legas kowace shekara, yana nuna hadin gwiwa mai kayatarwa tsakanin wasu masu hazaka da suka fi saurin tasowa a nahiyar Afirka. ART X na Kai-Tsaye! tsofaffin ɗalibai sun haɗa da Falana, WurlD, Lady Donli, Amaarae, TMXO, Odunsi the Engine, Wavy the Creator, da kuma Teni the Entertainer da mawakan zamani kamar Dafe Oboro, Joy Matashi, Williams Chechet, Drricky, Tunde Alara, Osaze Amadasun, Tomisin Akins, and Fadekemi Ogunsanya.
Dangane da karo na farko na kama-da-wane a na shekara ta 2020, wanda annoba ta duniya ta buƙata, ART X na Kai-Tsaye! farko Kamar Kallon Wani, ɗan gajeren fim ɗin wasan kwaikwayo wanda ke nuna mawaƙa Oxlade da Tomi Owó, mai zane na gani King Jesse Uranta, da DJ Camron waɗanda ke haɗa wasan kwaikwayo na bidiyo na kiɗa, hirarraki, zane-zane na dijital da saitin DJ, suna bincika duka nauyi da kuma damar ƙirƙirar a matsayin masu zane.[29]
Sautin fim ya haɗa da kiɗa ta Oxlade da Tomi Owó da kuma saitin da DJ Camron ya kirkira na juyin juya hali, kidan masu fafutuka, wanda ya kwashe shekaru da yawa a nahiyoyi da dama.[30]
Karo na shida na bikin, mai taken "Forward Ever", wasan kwaikwayo ne na kai tsaye da aka gudanar a ranar 6 ga watan Nuwamban 2021 kuma an kalle shirin duka a zahiri da kuma ta telebijin a kusan duk faɗin duniya, wanda Lanre Masha, Faridah Folawiyo da Ayo Lawson suka shirya, BigFoot da Pheelz ne suka shirya tare da nuna mawaƙa. Lojay, AYLØ, Dami Oniru tare da masu fasahar gani AMKMQ da Fez.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Freeman, Liam; Seb Emina (2018-10-30). "Why Lagos Is West Africa's Capital Of Culture". British Vogue. Retrieved 2019-03-08.
- ↑ "This Art Fair Is Basically The Frieze of West Africa". Harper's BAZAAR Arabia (in Turanci). Retrieved 2019-03-08.
- ↑ Proctor, Rebecca Anne (2019-11-05). "'The Idea Here Is to Go Big': Galleries at the Art X Lagos Fair Work to Cultivate Africa's Largest Economy". artnet News (in Turanci). Retrieved 2020-01-09.
- ↑ "Au Nigeria, un marché de l'art très prometteur" (in Faransanci). 2019-11-06. Retrieved 2020-01-09.
- ↑ "Africa's leading artists prepare for Lagos Fair - Premium Times Nigeria". Premium Times Nigeria (in Turanci). 2017-07-19. Retrieved 2018-01-16.
- ↑ 6.0 6.1 "Art X Lagos: west Africa's first international art fair". Financial Times (in Turanci). Retrieved 2018-03-29.
- ↑ Mitter, Siddhartha (2019-02-08). "Lagos, City of Hustle, Builds an Art 'Ecosystem'". The New York Times (in Turanci). ISSN 0362-4331. Retrieved 2019-03-08.
- ↑ "Lagos's lively arts scene". Apollo Magazine (in Turanci). 2018-11-29. Retrieved 2019-03-08.
- ↑ "CNN's African Voices meets Tokini Peterside, the founder of West Africa's first International Art Fair". My FrontPager. Archived from the original on 2018-05-22. Retrieved 2018-01-16.
- ↑ "The powerhouse behind Art X Lagos - CNN Video". Retrieved 2018-03-29.
- ↑ Amawhe, Oneme (2017-10-31). "Art X Lagos is a catalyst for West African art". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2018-01-16.
- ↑ 12.0 12.1 Editor, Online (2017-11-10). "For Art X the Future of Art in Africa is Stunning". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2018-01-16.CS1 maint: extra text: authors list (link)
- ↑ 13.0 13.1 Scott, Katy (2016-11-06). "Artists bend rules of contemporary African art". CNN Style (in Turanci). Retrieved 2021-12-01.
- ↑ Chutel, Lynsey (2017-10-30). "Art fairs may be nearing peak globally but in Africa they're just getting started". Quartz (in Turanci). Retrieved 2018-01-16.
- ↑ Das, Jareh (2020-12-19). "ART X Lagos Responds to #EndSARS". ocula.com (in Turanci). Retrieved 2020-12-19.
- ↑ 16.0 16.1 "Art X Lagos 2021 | West Africa's Premier Art Fair Returns". Latitudes Editorial (in Turanci). Retrieved 2021-11-29.
- ↑ Editor, Online (2017-08-13). "Art X to Showcase Africa's Leading Art Masters". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2018-01-16.CS1 maint: extra text: authors list (link)
- ↑ 18.0 18.1 "ART X Lagos returns with bigger and bolder ambitions - Ventures Africa". Ventures Africa (in Turanci). 2017-09-27. Retrieved 2018-01-16.
- ↑ Gbadamosi, Nosmot (2018-11-05). "$1.6 million painting first public display, and other highlights from ART X Lagos". CNN Style. Retrieved 2019-03-08.
- ↑ SamDuru, Prisca (2019-07-30). "Art X Lagos returns in November 2019". Vanguard News. Retrieved 2019-10-29.
- ↑ Adenike Olanrewaju (2020-12-09). "In the wake of tumultuous #EndSARS demonstrations, Nigerian photographers tell a story of strength and hope". CNN. Retrieved 2021-01-18.
- ↑ "ART X Talks 2020 - YouTube". www.youtube.com. Retrieved 2020-12-19.
- ↑ Rotinwa, Ayodeji (2021-11-05). "Art X Lagos puts NFTs by African artists in the limelight". The Art Newspaper. Retrieved 2021-11-29.
- ↑ Proctor, Rebecca Anne (2021-11-08). "'We Sell for the Same Prices Here That We Sell at Basel': Nigerian Collectors Hunt for West Africa's Next Art Stars at Art X Lagos". Artnet News. Retrieved 2021-11-29.
- ↑ Sam-Duru, Prisca; Vera Samuel Anyagafu (2017-10-03). "ART X LAGOS unveils galleries, artists for 2017 annual fair". Vanguard News. Retrieved 2018-05-13.
- ↑ "Art X Lagos returns with second edition, features 60 artists from 14 countries". Retrieved 2018-05-13.
- ↑ "Etinosa Yvonne wins 2019 Art X prize". The Guardian. Nigeria. 2019-09-21. Retrieved 2020-12-19.
- ↑ "Chigozie Obi wins N1.8m Access Bank Art X Prize - P.M. News". Retrieved 2021-11-29.
- ↑ "'Like Someone's Watching': A must see for 2020". Voice Online. 2020-12-11. Retrieved 2020-12-19.
- ↑ "Like Someone's Watching by ART X Live!". Apple Music. Retrieved 2020-12-19.