Best Ogedegbe
Best Ogedegbe (ranar 3 ga watan Satumban 1954 - ranar 28 ga watan Satumban 2009) shi ne mai tsaron ragar ƙwallon ƙafa ta Najeriya.
Best Ogedegbe | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Country for sport (en) | Najeriya |
Shekarun haihuwa | 3 Satumba 1954 |
Wurin haihuwa | Lagos, |
Lokacin mutuwa | 28 Satumba 2009 |
Wurin mutuwa | Jahar Ibadan |
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football manager (en) |
Matsayin daya buga/kware a ƙungiya | Mai tsaran raga |
Mamba na ƙungiyar wasanni | Shooting Stars SC (en) , Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya da Abiola Babes (en) |
Wasa | ƙwallon ƙafa |
Participant in (en) | 1980 Summer Olympics (en) , 1980 African Cup of Nations (en) da 1982 African Cup of Nations (en) |
Sana'a
gyara sasheYa buga wasa da Shooting Stars FC mafi yawan rayuwarsa, kuma shi ne mai tsaron gida a lokacin da Shooting Stars ta lashe kofin Nahiyar na farko a Najeriya, wato gasar cin kofin nahiyar Afirka a cikin shekarar 1976.
Ayyukan ƙasa da ƙasa
gyara sasheOgedegbe ya buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya wasa (a lokacin da ake kira "Green Eagles") lokacin da suka lashe gasar cin kofin ƙasashen Afirka a shekara ta 1980. Ya kuma wakilci Najeriya a gasar Olympics ta bazara a shekarar 1980 a birnin Moscow.
Aikin koyarwa
gyara sasheOgedegbe mataimakin koci ne a lokacin kakar 2008 – 09 na Dolphins FC [1] Ya kuma kasance tsohon mataimaki tare da Wikki Tourists da kuma ƙungiyar masu lambar azurfa ta shekarar 2008 Summer Olympics.
Mutuwa
gyara sasheYa rasu yana da shekaru 55 a Asibitin Kwalejin Jami’ar Ibadan a ranar 28 ga watan Satumban 2009. An yi masa tiyatar ido ne a makon da ya gabata, amma ya shiga suma bayan da aka samu matsala daga aikin. [2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Ogedegbe dreams double laurels with Dolphins[permanent dead link]
- ↑ Christian Okpara, Iyabo Lawal (Ibadan) and Olalekan Okusan: Green Eagles goalkeeper, Ogedegbe dies at 55[permanent dead link], The Guardian (Nigeria), 29 September 2009.