Baure (Nijeriya)

Ƙaramar hukuma ce a Nigeria

Baure Karamar Hukuma ce da ke a Jihar Katsina, Arewa maso yammacin Nijeriya.

Baure

Wuri
Map
 12°47′00″N 8°46′00″E / 12.7833°N 8.7667°E / 12.7833; 8.7667
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJahar Katsina
Labarin ƙasa
Yawan fili 707 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Baure Gari ne da ke ƙarƙashim masarautar Daura kuma yana gabashin Daura[1]. ƙaramar hukuma ce a garin katsina mai zaman kanta wacce a ka samar da ita a shekarar ta alif dari tara da casa'in da shida 1996[1].

Dangane da kafuwar garin Baure masana tarihi sun nuna cewa a zamanin Sarkin Daura Lukudi (1825 – 1855) aka fara kafa ta, dalilin ‘ya’yan sarki da suka yi tawaye suka kafa garuruwa a babban Birnin Daura sannan suka ɗaura kan su matsayin sarakuna[1]. wanda ɗaya daga cikin ƴa’ƴan Sarkin ya sauka a wannan wuri da jama’arsa suka sauka gindin wani ƙaton Ɓaure suka yada zango sukai ta taruwa ta haka ne aka riƙa kiran wajen da suna “Ɓaure”[1].

Fulani sun ƙwace haɓen Daura, da Baure da kanta a lokacin jihadin Usman Ɗan Fodio, a ƙarƙashin Jagorancin “Malam Musa”. Bayan isowar turawa arewacin Najeriya suka karɓe mulkin daga hannun fulani a shekarar 1903. Daga nan turawa suka kashe wancen ƙananan garuruwan da ƴa’ƴan sarki suka kafa kuma suka kafa garin Daura kaɗai[1].

A yanzu garin Ɓaure ya samu ci gaba a fanni daban daban, kama daga harkar ilimi, noma, da kiwo, da karkar kula da lafiya. Garin Ɓaure yayi fice a sana’o’in gargajiya[2].

Shuwagabanni

gyara sashe

Wasu daga cikin Hakiman Ɓaure da aka yi sun Haɗa da:

1-   Ƙauran Ɓaure Aasan

2-    Ƙaura Umaru Sanda

3-   Ƙaura Hamis

4-   Ƙaura Muhammadu turno

5-   Ƙaura Hamisu Abubakar[3].

Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. ISBN 978-2105-93-7. OCLC 59226530.

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.11. ISBN 978-2105-93-7.
  2. Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.12. ISBN 978-2105-93-7.
  3. Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.14. ISBN 978-2105-93-7.