Balaraba Ramat Yakubu kwarariyar marubuciyar littattafan Hausa ce da ake wa laƙabi littattafan soyayya. An haife ta a cikin birnin Kano a a shekara ta alif ɗari tara da hamsin da tara 1959A.c[1] . Tana daga kalilan marubuta da aka fassara littafinta zuwa harshen Inglishi. Rubuce - rubucenta sun fi bada muhimmanci akan zamantakewar aure da kuma gwagwarmayar mata a rayuwar Hausawa, musamman tauye hakkin mata da mazan Hausawa kan yi, zamu ga haka a littattafan ta kamar Budurwar zuciya da mashahurin littafin ta Alhaki kuikuyo ne.

Balaraba Ramat Yakubu
Rayuwa
Haihuwa jahar Kano, 1959 (64/65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Ahali Murtala Mohammed
Karatu
Harsuna Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a marubuci
Balaraba Ramat Yakubu

Kuruciyarta

gyara sashe

Hajiya Balaraba kanwa ce ga tsohon shugaban kasar Nijeriya, marigayi Murtala Ramat Muhammed wanda aka yi wa juyin mulki a shekarar 1976.

Tun tana karama 'yar shekara 13 aka cire ta daga makaranta aka yi mata aure, wannan ne ma dalilin da ya sa take rubuce - rubucent da harshen Hausa maimakon turanci.[2]

 
Budurwar Zuciya

Balaraba Ramat ta kasance mace tilo a cikin jagororin kungiyar marubuta mai suna  Raina Kama.[3]  Littafinta na farko shi ne  Budurwar Zuciya wanda aka wallafa a shekarar 1987. Daga nan ta ci gaba da rubuce - rubuce har zuwa daga bisani ta shiga harkar rubutun fim tare da shiryawa. A shekarar 1998, Muhammed Abdulkareem ya mayar da littafinta,  Alhaki Kwikwiyo Ne zuwa fim 1998.[4]

Har ila yau kuma, a shekarar 2012, wani kamfanin dab'i a kasar Indiya mai suna Blaft Publishers ya wallafa fassarar littafin Alhaki Kwikwiyo Ne zuwa Inglishi. Littafin ya samu kyakkyawan yabo [5][6] Daga cikin littattafan ta akwai: Wa zai auri jahila? 1-2, Ina son sa haka (an mayar da shi fim), Matar uba Jaraba, Wane kare ne, ba kare?, Badariyya 1-5 da sauran su. Amma dai gaskiya littafin Alhaki kuikuyo yafi kowanne ɗaukan hankali. Lami Sumayya Murtala ta gidan rediyon DW sun taba karanta littafin a audio. An samar da wasu kyaututtuka ga matasan marubuta wanda aka rada wa kyautar sunan Balaraba Ramat Yakubu.[7]

Manazarta

gyara sashe
  1. Femke van Zeijl, "From illiterate child bride to famous Nigerian novelist", Al Jazeera (Features), 8 March 2016.
  2. "I write in Hausa 'cos I didn't get Western education - Says Murtala Muhammed's sister". NigeriaFilms.com. Archived from the original on 23 April 2016. Retrieved 11 January 2013.
  3. Graham Furniss. "Hausa popular literature and video film: the rapid rise of cultural production in times of economic decline" (PDF). Archived from the original (PDF) on 16 July 2016. Retrieved 11 January 2013.
  4. Carmen Mccain (22 October 2012). "Hajiya Balaraba Ramat Yakubu's novel Alhaki Kuykuyo Ne/Sin is a Puppy Published in translation by Blaft". Retrieved 11 January 2013.
  5. Subashini Navaratnam (6 December 2012). "'Sin is a Puppy That Follows You Home', a Popular Hausa Novel, Is a Fast-Paced, Riveting Read". Retrieved 11 January 2013.
  6. Deepa Dharmadhikari. "Book Review: Full Hausa". Retrieved 11 January 2013.
  7. Awaal Gaata. "CATCHING THEM YOUNG: School gives prizes to students in Kano". Archived from the original on 15 February 2013. Retrieved 11 January 2013.