Baffa Babba Danagundi

Dan siyasar Nigeria

Baffa Babba Danagundi, anfi saninsa da Baffanyo, dan siyasa ne daga Jihar Kano, Nigeria, shine tsohon shugaban masu rinjaya ye a Majisar Jihar Kano.[1][2][3]

Baffa Babba Danagundi
member of the Kano State House of Assembly (en) Fassara

2015 -
Rayuwa
Haihuwa Kano Municipal, 22 ga Yuni, 1973 (51 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Kano
Jami'ar Bayero
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Baffa Babba Danagundi dai an haife shi ne a Kofar Danagundi quarters dake Kano Municipal a shekara ta 1973. Shi dan dangin Babba Danagundi ne, wanda yake daga cikin masu nadin sarki a Majalisar Masarautar Kano, yana da nadin Sarkin Dawaki Mai Tuta kuma jika ne ga Jamo dan Sullubawan Fulani.

Baffa yayi makarantar Gidan Makama Special Primary School daga shekara ta 1981 zuwa 1986, sannan yayi Government Technical College, Wudil daga 1986 zuwa 1989, da kuma Unity College, Karaye daga 1989 zuwa 1992. Baffa yayi karatun National Diploma da Higher National Diploma daga Kano State Polytechnic. Baffa kuma yana da shaidar MBA daga Bayero University Kano.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Majority Leader". Kano State Assembly (in Turanci). 2017-08-30. Archived from the original on 2021-01-21. Retrieved 2021-02-10.
  2. "Baffa Babba". Kano State Assembly (in Turanci). 2018-02-24. Archived from the original on 2021-01-26. Retrieved 2021-02-10.
  3. "Ganduje Declared Winner In Kano, As APC Sweeps State Assembly". Channels Television. Retrieved 2021-02-04.