Baure (Nijeriya)
Baure Karamar Hukuma ce da ke a Jihar Katsina, Arewa maso yammacin Nijeriya.
Baure | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jahar Katsina | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 707 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Baure Gari ne da ke ƙarƙashim masarautar Daura kuma yana gabashin Daura[1]. ƙaramar hukuma ce a garin katsina mai zaman kanta wacce a ka samar da ita a shekarar ta alif dari tara da casa'in da shida 1996[1].
Tarihi
gyara sasheDangane da kafuwar garin Baure masana tarihi sun nuna cewa a zamanin Sarkin Daura Lukudi (1825 – 1855) aka fara kafa ta, dalilin ‘ya’yan sarki da suka yi tawaye suka kafa garuruwa a babban Birnin Daura sannan suka ɗaura kan su matsayin sarakuna[1]. wanda ɗaya daga cikin ƴa’ƴan Sarkin ya sauka a wannan wuri da jama’arsa suka sauka gindin wani ƙaton Ɓaure suka yada zango sukai ta taruwa ta haka ne aka riƙa kiran wajen da suna “Ɓaure”[1].
Fulani sun ƙwace haɓen Daura, da Baure da kanta a lokacin jihadin Usman Ɗan Fodio, a ƙarƙashin Jagorancin “Malam Musa”. Bayan isowar turawa arewacin Najeriya suka karɓe mulkin daga hannun fulani a shekarar 1903. Daga nan turawa suka kashe wancen ƙananan garuruwan da ƴa’ƴan sarki suka kafa kuma suka kafa garin Daura kaɗai[1].
A yanzu garin Ɓaure ya samu ci gaba a fanni daban daban, kama daga harkar ilimi, noma, da kiwo, da karkar kula da lafiya. Garin Ɓaure yayi fice a sana’o’in gargajiya[2].
Shuwagabanni
gyara sasheWasu daga cikin Hakiman Ɓaure da aka yi sun Haɗa da:
1- Ƙauran Ɓaure Aasan
2- Ƙaura Umaru Sanda
3- Ƙaura Hamis
4- Ƙaura Muhammadu turno
5- Ƙaura Hamisu Abubakar[3].
Biblio
gyara sasheTarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. ISBN 978-2105-93-7. OCLC 59226530.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.11. ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.12. ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.14. ISBN 978-2105-93-7.