Arewacin Cyprus

ƙasa a kan tsibirin Cyprus

Arewacin Cyprus ( Turkish ), a hukumance Jamhuriyar Turkiyya ta Arewacin Cyprus ( TRNC ; Turkish , KKTC ), yanki ne na zahiri a arewacin rabin tsibirin Cyprus. Mutane dubu ɗari uku suna rayuwa a cikin 3,335 km² Turkiyya ce kaɗai ƙasar da ta amince da yankin a matsayin jamhuriya mai cin gashin kanta duk da takunkumin ƙasa da ƙasa da ake sakawa.

Arewacin Cyprus
Kuzey Kıbrıs Türk Cumhuriyeti (tr)
Flag of Northern Cyprus (en) Coat of arms of Northern Cyprus (en)
Flag of Northern Cyprus (en) Fassara Coat of arms of Northern Cyprus (en) Fassara

Take İstiklâl Marşı (en) Fassara

Wuri
Map
 35°11′N 33°22′E / 35.18°N 33.36°E / 35.18; 33.36
Territory claimed by (en) Fassara Cyprus

Babban birni North Nicosia (en) Fassara
Yawan mutane
Faɗi 390,745 (2021)
• Yawan mutane 116.47 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turkanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 3,355 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Turkish Federated State of Cyprus (en) Fassara
Ƙirƙira 1983
Tsarin Siyasa
Gangar majalisa Assembly of the Republic (en) Fassara
• President of Northern Cyprus (en) Fassara Ersin Tatar (en) Fassara (23 Oktoba 2021)
• Prime Minister of Northern Cyprus (en) Fassara Ünal Üstel (en) Fassara (12 Mayu 2022)
Ikonomi
Kuɗi Turkish lira
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
UTC+02:00 (en) Fassara
Suna ta yanar gizo .tr (mul) Fassara
Tsarin lamba ta kiran tarho +90
Lambar taimakon gaggawa *#06#
File:View over Girne from Kyrenia Castle - Girne (Kyrenia) - Turkish Republic of North Cyprus
File:Coat of arms of the Turkish Republic of Northern Cyprus
bakin teku

An ci Cyprus da yaƙi kuma ta zama wani ɓangare na Daular Usmaniyya daga shekarar 1570-1914. Turkawa da yawa sun zama baƙi . Yayin da Daular Ottoman ta goyi bayan daular Birtaniyya a yaƙin duniya na daya, Turawan Burtaniya suka mamaye Cyprus. A cikin 1923, ta Yarjejeniyar Lausanne Turkiyya ta ba da tsibirin ga Masarautar Burtaniya wanda a cikin 1925 ya mai da shi ya zama masarautar mallaka . Birtaniyyawan sun mallake shi daga 1878 har zuwa 1960.

A cikin 1974, don mayar da martani ga wani rikici da ke ƙaruwa da Girka, sojojin Turkiyya sun mamaye Cyprus. Yawancin baƙi daga asalin Turkiyya sun fito daga Turkiyya zuwa arewacin tsibirin. Wannan matakin ya jawo Allah wadai daga kasashen duniya kuma Majalisar Dinkin Duniya ba ta amince da Arewacin Cyprus ba.

Tun daga shekarar 1974, Majalisar Ɗinkin Duniya ta kafa layin tsagaita wuta tsakanin Tsibirin Cyprus na Turkiya da Girkawan Cyprus. An kafa '' Jamhuriyar Turkiyya ta Arewacin Cyprus '' a cikin 1983 kuma Rauf Denktash ya zama shugaban ƙasa na farko. An gudanar da shawarwari game da hadadden tsibiri sau da yawa ba tare da nasara ba.

jami ar Cyprus
bakin ruwan Cyprus
chochi a Cyprus

Arewacin Cyprus, duk da matsayin da take da shi na kasashen duniya, ya yi fice a tsakanin sauran yankunan "daskararrun rikice-rikice" kamar yadda yake da kyakkyawan tsarin mulki na dimokiradiyya tare da manyan matakan 'yanci na siyasa da kuma shiga tsakani a harkar siyasa.

Sauran yanar gizo

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe