Alhaji Ali (kuma Ali dan Umar ) shi ne Mai (Sarki) na daular Bornu, a yanzu kasashen Afirka ne na Chadi, Najeriya, da Nijar, suke sashin Daular, daga 1639 zuwa kusan 1680. Ali ya gaje mahaifinsa Umar a shekara ta 1639 kuma ya samu doguwar sarauta. A farkon shekarun mulkinsa, ana yi wa daular barazanar kutsen hari daga makwabta, sune yan Tuareg a arewa da Kwararafa a kudu. Ya sami damar riƙe duka runduna biyun a filin daga, daga ƙarshe ya ci su da yaki a 1668. Bayan nasarar sa, ya ƙarfafa mulkinsa, ta hanyar kula da muhimman hanyoyin kasuwancin Saharan, da kuma sake koyar da addinin Islama a daular. Ana tuna shi da irin taka rawarsa, da ya gina masallatai guda hudu da kuma yin hajji guda uku a gari mai tsarki Makka .

Ali II na Bornu
Rayuwa
Haihuwa unknown value
ƙasa Bornu Empire (en) Fassara
Mutuwa 1680
Sana'a

Diddigin bayanai gyara sashe

  • HJ Fisher. "Sahara da Sudan ta Tsakiya" a cikin Tarihin Kambik na Afirka: Daga c.1600 zuwa c.1790 . Richard Gray, JD Fage, Roland Anthony Oliver, eds. Jami'ar Cambridge, (1975)