Ali Ahmad Mullah
Ali Ahmad Mullah (An haife shi a ranar 5 ga watan Yuli shekarar 1945), shi gogaggen mai wazana ne (mai kiran sallah/Ladanci) a Masallacin Ka'aba (Masjid al-Haram) a Makka, Saudiyya tsawon shekaru talatin da suka gabata.[1][2][3] Ali Ahmad Mullah shi ne Ladanin da ya fi kowa daɗewa yana kiran Sallah a Masallacin Harami wannan kusan ace al’adar gidan su ne a wannan sana’a tun a shekarar 1975.[4]
Ali Ahmad Mullah | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Makkah, 5 ga Yuli, 1945 (79 shekaru) |
ƙasa | Saudi Arebiya |
Harshen uwa | Larabci |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | ladani |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Al'ummar Musulmi na girmama shi a duk fadin duniya, kuma sautin muryarshi yana burge mutane, suna jin daɗin kiran Sallah shi a duk fadin duniya Musulmai da waɗanda ba Musulmai ba ta kafafen yaɗa labarai iri daban-daban. Ya kuma bayyana cewa babban aikinsa banda Ladanci a masallacin harami shi ne yin sana’arsa ta kasuwancin sa. Ya yi aure sau 4 yana da ƴaƴa 3 da kowace mace. Ɗansa, Atef bin Ali Ahmad Mullah, yanzu yana ci gaba da aikin yana kuma halartarci Masjid-al-Haram a ranar 4 ga Afrilu 2022.
Sana'a da Karatu
gyara sasheAli Ahmad Mullah ya fara kiran Sallah ne a masallacin yana ɗan shekara 14, yana kiran sallah daga majami'u a lokacin da babu Abdul Hafeez Khoja, da kawun mahaifiyarsa, Abdul Rahman Mullah, kawun mahaifinsa, da Ahmad Mullah, kakansa, waɗanda dukkansu ladanai ne a masallaci. Mullah ya fara gabatar da kiran Sallah tun lokacin da babu lasifika, a lokacin da masu kiran Sallah suke hawa daga cikin hasumiya guda bakwai kamar su Bab Al-Umrah Minaret, Bab Al-Ziyara Minaret, da Bab Al-Hekma Minaret, don kiran Sallah. Shugaban ladanan Al-Shafie Maqam, kusa da rijiyar zamzam yake gabatar da wazana ɗin, daga nan kuma kowane Ladani ya maimaita abin da yaji babban ladan na farko ya ce har sai an kammala wazana ɗin. Al'ada ce da Daular Usmaniyya ta fara, wadda a yau ake ci gaba da yi a ƙasar Turkiyya. Bayan kammala karatunsa a Cibiyar Ilimin Fasaha da ke Riyadh a shekarar 1970, Mulla ya yi aiki a matsayin malami a makarantar Abdullah ibn Al-Zubair ''Intermediate School''. An naɗa shi a matsayin Ladan a hukumance a Masallacin Harami a shekarar 1984. Ya kuma samu karramawa da yin kiran Sallah a Masallacin Al-Nabawi da ke Madina a wani lokaci. Yin Ladanci a Masallacin Harami, ga musulmi masallaci mafi tsarki a duniya, ya yi iƙirarin cewa duk wanda ya samu damar kasancewa cikin masu kiran Sallah a wannan masallaci, ya kai matsayi babba kuma abin girmamawa.
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ Batool, Zehra (2021-07-17). "Sheikh Ali Ahmed Mulla, The 'Bilal' Of Grand Mosque Is The Voice You've Been Hearing For 4 Decades!". Parhlo (in Turanci). Retrieved 2021-09-13.
- ↑ "'Bilal' - muezzin of Grand Mosque of Mecca for four decades" (in Turanci). 2018-05-24. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "FaceOf: Sheikh Ali Ahmad Mulla, muezzin of the Grand Mosque in Makkah". Arabnews.com. Arabnews. Retrieved 30 September 2020.
- ↑ "কাবা শরিফের প্রবীণ মুয়াজ্জিনের কণ্ঠে আজান যেমন | কালের কণ্ঠ". Kalerkantho (in Bengali). 2021-09-06. Retrieved 2021-09-13.