Alex Egbona
Alex Egbona (an haife shi a 15 ga watan Oktoba, 1964) ɗan siyasan Najeriya ne. Kuma ɗan majalisar wakilan tarayyar Najeriya ne mai wakiltar mazaɓar Yakurr/Abi a jihar Cross River.[1] An naɗa shi mataimaki na musamman, na ayyuka na musamman ga Gwamnan Jihar Kuros Riba na lokacin sannan kuma ya naɗa shi mataimakin shugaban ma’aikata da kuma mamba a majalisar zartarwa ta jihar Cross River. [2]
Alex Egbona | |||||
---|---|---|---|---|---|
29 ga Janairu, 2020 - District: Yakurr/Abi
11 ga Yuni, 2019 - 2 Nuwamba, 2019 District: Yakurr/Abi | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 15 Oktoba 1964 (60 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Egbona a ranar 15 ga watan Oktoba, 1964, kuma ya girma a Agbara Ekureku. Ya yi makarantar firamare a ƙaramar hukumar Abi ta jihar. [2] Daga shekarun 1975 zuwa 1982, Egbona ya halarci makarantar Agbo Comprehensive School. Ya samu takardar shedar Sakandare a Kwalejin Fasaha da Kimiyya da ke Ogoja. [3] A shekarar 1990 ya samu digirin digirgir a fannin tattalin arziki a jami'ar Fatakwal sannan ya kammala hidimar ƙasa ta tilas a jihar Kaduna. [3]
A shekarar 1996, Egbona ya samu digiri na biyu a fannin harkokin gwamnati a jami’ar Calabar sannan kuma ya yi digiri na biyu a fannin tsare-tsare na ilimi. [4] A watan Fabrairun 2014, ya sami digiri na Doctor of Philosophy (PhD) a fannin Gudanar da Ilimi da Tsare-tsare tare da Sha'awa ta Musamman akan Tsarin Siyasa da Aiwatarwa daga Jami'ar Calabar. [4]
Sana'a
gyara sasheEgbona ya taɓa zama mataimaki na musamman ga Donald Duke, Gwamnan Jihar Kuros Riba a lokacin daga shekarun 2002 zuwa 2003. [4] Daga nan ya zama shugaban ma’aikata ga Sanata Liyel Imoke, Gwamnan Jihar Kuros Riba a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2014. [5] [6] [7]
Egbona ya ci zaɓe a karo na biyu a majalisar dokokin ƙasar kuma ya zama ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Yakurr/Abi. [8] [9]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Egbona, Alex. "NASS Legislators". nass.gov.ng.
- ↑ 2.0 2.1 Igboke, Stanley Patrick (28 September 2014). "the-alex-egbona-that-people-do-not-know". Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "Calitown" defined multiple times with different content - ↑ 3.0 3.1 "Unveiling Hon. Alex Egbona, PhD – Alex Egbona" (in Turanci). 12 August 2020. Retrieved 2023-04-30.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 "about-alex". 12 August 2020. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "self" defined multiple times with different content - ↑ Eguzozie, Ben (26 October 2014). "My representation will usher in new lease of life for my constituents – Egbona".
- ↑ tnnonline (2020-01-29). "After Historic Victory, Egbona Says He Has Forgiven Those Who Opposed Him… Says Imoke Remains His Master -Egbona | TNN Newspaper" (in Turanci). Retrieved 2023-04-30.
- ↑ Admin (2015-11-04). ""Imoke Told Alex Egbona To Run For House Of Reps" – Chuks Agube". calitown (in Turanci). Retrieved 2023-04-30.
- ↑ "Egbona, C'River Rep, wins second term election".
- ↑ Online, The Eagle (2023-02-27). "Alex Egbona wins reelection as Reps Member -". The Eagle Online (in Turanci). Retrieved 2023-04-30.