Akwasi Konadu
Akwasi Konadu dan siyasan Ghana ne wanda mamba ne a New Patriotic Party (NPP).[1][2] Shi ne dan majalisa mai wakiltar mazabar Manhyia ta Arewa a yankin Ashanti na Ghana.[3] A halin yanzu shi ne Darakta a kamfanin Ghana Water Company Limited.[4]
Akwasi Konadu | |||||
---|---|---|---|---|---|
2022 -
7 ga Janairu, 2021 - District: Manhyia North Constituency (en) Election: 2020 Ghanaian general election (en) | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Yankin Ashanti, 25 ga Yuli, 1982 (42 shekaru) | ||||
ƙasa | Ghana | ||||
Harshen uwa | Yaren Asante | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Opoku Ware Senior High School (en) Jami'ar Ilimi, Winneba diploma (en) : education (en) University of Ghana Bachelor of Arts (en) : kimiyar al'umma, falsafa Kwame Nkrumah University of Science and Technology Master of Science (en) : development policy (en) , planning (en) | ||||
Harsuna |
Turanci Yaren Asante | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da supervisor (en) | ||||
Wurin aiki | Kumasi | ||||
Imani | |||||
Addini | Kiristanci | ||||
Jam'iyar siyasa | New Patriotic Party |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Konadu a ranar 25 ga watan Yuli shekara ta, 1982 kuma ya fito ne daga Paakoso a yankin Ashanti. Ya yi karatunsa na sakandare a Opoku Ware Secondary School. Ya sami Diploma a fannin Ilimi daga Jami'ar Ilimi - Winneba. Ya kuma yi digirinsa na farko a fannin zamantakewa tare da Falsafa a shekarar, 2005 daga Jami'ar Ghana. Sannan kuma ya samu digirin sa na biyu (Masters) a fannin siyasa da tsare-tsare daga KNUST.[4][5]
Aiki
gyara sasheKonadu shi ne Mataimakin Auditor na KDA Accounting Services a Kumasi. Ya kuma kasance jami'in kula da ayyukan gidauniyar Bonsafo Barwuah. Ya kasance Manajan Ayyuka na Kamfanin Greenfield Limited.[5]
Siyasa
gyara sasheKonadu ya shiga takarar ɗan majalisa a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar NPP a mazaɓar Manhyia ta Arewa gabanin zaben shekara ta, 2020.[6][7][8] Ya tsige dan majalisar mai ci Collins Owusu Amankwah, wanda ya taba zama majalisar tun daga watan Janairun shekara ta, 2013, a wata fafatawar da aka yi a watan Yunin shekara ta, 2020 domin zama ɗan takarar jam’iyyar da zai wakilci mazabar Manhyia ta Arewa a zaben shekara ta, 2020.[9][10] Ya samu nasara ne bayan ya samu ƙuri'u, 278 yayin da mai ci ya samu ƙuri'u, 273 inda ya doke shi da kuri'u 5.[1][11][12] Kafin nasarar Konadu ya yi takara a zaben fidda gwani na shekara ta, 2012 da na 2016 da Collins Owusu Amankwaah kuma ya sha kashi a duka lokutan biyun.[13]
An zaɓi Konadu dan majalisa mai wakiltar Manhyia North a zaben majalisar dokoki na Disamba 2020. An ayyana shi ne a matsayin wanda ya lashe zaben ‘yan majalisar dokokin kasar bayan ya samu ƙuri’u 39,562 da ke wakiltar kashi 69.9 cikin 100, yayin da dan takararsa na jam’iyyar National Democratic Congress, Hamza Swallah ya samu ƙuri’u 15,943 da ke wakiltar kashi 28.2%.[3]
Kwamitoci
gyara sasheKonadu mamba ne a kwamitin dabarun rage talauci kuma mamba ne a kwamitin lafiya.[5]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Manhyia North: Akwasi Konadu unseats Owusu Amankwah with 5 votes". www.ghanaweb.com (in Turanci). 2020-06-20. Retrieved 2021-01-06.
- ↑ "NPP Primaries: Akwasi Konadu confident of winning Manhyia North contest". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana (in Turanci). 2020-02-16. Retrieved 2021-01-06.
- ↑ 3.0 3.1 FM, Peace. "2020 Election - Manhyia North Constituency Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2021-01-06.
- ↑ 4.0 4.1 "HON. AKWASI KONADU – GWCL – Welcome" (in Turanci). Retrieved 2022-08-19.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 5.3 "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 2022-08-19.
- ↑ "NPP primaries: Deputy Speaker, Majority Leader, 12 others go unopposed". MyJoyOnline.com (in Turanci). Retrieved 2021-01-06.
- ↑ "Education Sector Will Win NPP Power". DailyGuide Network (in Turanci). 2020-07-14. Retrieved 2021-01-06.
- ↑ "Anti-LGBTQ Bill will end decades of moral decadence - Manhyia North MP - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). 2021-07-27. Retrieved 2022-08-19.
- ↑ "List of 'fallen' MPs after NPP parliamentary primaries". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana (in Turanci). 2020-06-20. Retrieved 2021-01-06.
- ↑ "NPP Big Guns Fall 7 Ministers Out!". DailyGuide Network (in Turanci). 2020-06-22. Retrieved 2021-01-06.
- ↑ "#NPPDecides: 10 incumbent MPs in Ashanti Region lose primaries". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana (in Turanci). 2020-06-21. Retrieved 2021-01-06.
- ↑ "NPP Primaries: Akwasi Konadu beats Owusu Amankwah with 5 votes". The Ghana Guardian News (in Turanci). Retrieved 2022-08-19.
- ↑ "Manhyia North: Who gets the nod... Amankwah or Konadu?". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2021-01-06.
- ↑ "Konadu, Akwasi". Ghana MPS (in Turanci). Retrieved 2022-08-19.