Agatha Christie
Dame Agatha Mary Clarissa Christie, Lady Mallowan, DBE (née Miller; 15 Satumba 1890 - 12 Janairu 1976) marubuciyar birtaniya ce wacce aka sani da litattafan bincikenta 66 da tarin gajerun labarai 14, musamman waɗanda ke juyawa kan almara Hercule Poirot da Miss Marple. Ta kuma rubuta wasan kwaikwayo mafi tsayi a duniya, sirrin kisan kai The Mousetrap, wanda aka yi a West End tun 1952. Marubuciyar, a lokacin "Golden Age of Detective Fiction", Christie an kira ta "Sarauniyar Laifi". Ta kuma rubuta litattafai shida a ƙarƙashin sunan Mary Westmacott. A cikin 1971, Sarauniya Elizabeth ta biyu ta yi mata karramawar Dame (DBE) saboda gudummawar da ta bayar ga adabi. Guinness World Records ta lissafta Christie a matsayin marubucin almara wacce labaranta suka sayu matuqa a kowane lokaci, litattafanta sun sayar da fiye da kwafi biliyan biyu.[1][2]
Tasowarta
gyara sasheAn haifi Christie a cikin wani dangi na babban attajiri a Torquay, Devon, mai tsarin karatun-gida. Da farko ita marubuciya ce da ba ta yi nasara ba tare da kin amincewa shida a jere, amma wannan ya canza a cikin 1920 lokacin da aka buga The Mysterious Affair at Styles, wanda ke nuna jami'in binciken Hercule Poirot. Mijinta na farko shine Archibald Christie; sun yi aure a shekara ta 1914 kuma sun haifi ɗa guda kafin su sake aure a shekara ta 1928. Bayan rushewar aurenta da rasuwar mahaifiyarta a 1926 ta shiga kanun labaran duniya ta hanyar bata kwana goma sha ɗaya. A lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, ta yi hidima a ma'aikatun asibiti, ta sami cikakkiyar masaniya game da gubar da ke cikin yawancin litattafanta, gajerun labarai, da wasan kwaikwayo. Bayan aurenta da masanin ilimin kimiya na kayan tarihi Max Mallowan a 1930, ta shafe watanni da yawa a kowace shekara a kan tono a Gabas ta Tsakiya kuma ta yi amfani da iliminta na farko na wannan sana'a a cikin almara.[3][4]