Afia Efere
Afia Efere miyar Najeriya ce da ta shahara a tsakanin kabilar Efik, miyar kuma ana kiranta da farar miya saboda ba a yinta da manja.[1][2]
Afia Efere | |
---|---|
miya | |
Kayan haɗi | naman akuya, crayfish (en) , doya, seasoning (en) , gishiri, ruwa, stockfish (en) da Peppered Ponmo (en) |
Tarihi | |
Asali | Najeriya |
Asali
gyara sasheFarar miya ta samo asali ne daga kabilar Efik kuma tana kama da miyar Inyamurai 'Ofe Nsala' sai dai ana amfani da kayan miya kadan wajen yinta kuma ita Ofe Nsala ba a yinta da uyayak, maimakon haka Ofe Nsala' ana yinta ne da Utazi da Ogiri. Mutanen Calabar galibinsu kabilar Efik ne.[3]
Bayani
gyara sasheMiyar wanda ba’a yinta da mai ana yinta ne da nama nau’i biyu naman akuya ko kaza kuma wannan shine dalilin da ysa ake kiranta da wasu sunayen kamar "Afiaefereebot" kuma "afiaefereunen" ma'ana farar miya da akuya da kuma farar miya da kaza.[4]
Sauran sinadaran da ake amfani da su wajen hada miyar sun hada da uyayak, Ehu (Calabash nutmeg), ganyen uziza, crayfish da da makamantansu
Duba kuma
gyara sashe- Nsala miyar
- Ikot Udo Abia
Manazarta
gyara sashe- ↑ "How to Make Afia Efere In One Hour". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2018-04-15. Archived from the original on 2022-06-29. Retrieved 2022-06-29.
- ↑ "Afia Efere". ResearchGate.
- ↑ "I grew up eating fresh food - Ijeoma Onwudiwe". Vanguard News (in Turanci). 2011-06-17. Retrieved 2022-06-29.
- ↑ isaac (2013-12-12). "Dishes You Must Try Out In Calabar". Pulse Nigeria. Retrieved 2022-06-29.