Abdulfatai Yahaya Seriki
,
Abdulfatai Yahaya Seriki | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jos, 8 Oktoba 1978 (46 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Yahaya Seriki (An haife shi a ranar 8 ga watan Oktoba, shekara ta alif dari tara da saba'in da biyar 1975) [1] jigon jam’iyyar APC ne daga Ilorin Jihar Kwara a Arewacin Najeriya . Kafin shiga harkar siyasa, Yahaya Seriki hamshakin ɗan kasuwa ne kuma mai taimakon jama’a wanda ke mai da hankali kan talakawa da masu fama da nakasa. Shi ne wanda ya kafa kuma Manajan Darakta na Kursi Investments Limited.[2][3]
Rayuwar farko.
gyara sasheAn haife shi a Kaduna, ya taso a Maiduguri da Jos ;babban birnin mulki kuma mafi girma a jihar Filato.
Siyasa.
gyara sasheAbdulFatai Yahaya Seriki Gambari dai tsohon ɗan takarar gwamna ne na jam'iyyar APC a zaɓen gwamna na 2019 a jihar Kwara sannan kuma jigo ne a jam'iyyar APC a jihar Kwara. Shi ne ɗan takara na farko da ya sauka domin nuna goyon bayansa ga gwamna mai ci Abdrahman Abdulrasaq.
Ya taɓa zama Darakta Janar na yaƙin neman zaben da ya samar da Gwamnan Jihar Kwara Abdulrahman Abdulrasaq. Shi dai fitaccen ɗan kungiyar ‘O To Ge’ ne da ya ruguza siyasar tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki [4] in Kwara state. [5]
Rayuwa ta sirri.
gyara sasheYana auren Fatimah Abdulfatah kuma ma'auratan suna da ƴa ƴa maza hudu.
Manazarta.
gyara sashe- ↑ "You are being redirected..."
- ↑ "Management". Archived from the original on 2021-06-11. Retrieved 2023-10-24.
- ↑ "Reference at www.latestschgist.com.ng". Archived from the original on 2022-12-06. Retrieved 2023-10-24.
- ↑ Bukola Saraki
- ↑ Ó Tó Gẹ́